‘Dawo da Tallafin Mai a Ɓoye’: Jigon PDP ya Buƙaci Tinubu Ya Faɗa wa Yan Najeriya Gaskiya

‘Dawo da Tallafin Mai a Ɓoye’: Jigon PDP ya Buƙaci Tinubu Ya Faɗa wa Yan Najeriya Gaskiya

  • Tsohon mataimakin shugaban PDP na kasa, Bode George ya buƙaci Bola Tinubu ya faɗawa yan Najeriya gaskiya kan cire tallafin mai
  • Bode George ya ce akwai ruɗani kan yadda ake maganar cewa gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin man fetur ta bayan fage
  • Haka zalika Bode George ya yi magana kan aniyar gwamnatin Bola Tinubu na sayarwa matatar Dangote danyen mai da Naira

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Bode George ya yi kira na musamman kan cire tallafin man fetur.

Bode George ya yi magana ne kan yadda ruɗani ya kewaye maganar cewa gwamnatin tarayya ta dawo da tallafin mai a ɓoye kwanaki.

Kara karanta wannan

Tinubu ya ƙara daukan matakin ragewa talaka raɗaɗin cire tallafin man fetur

Bode George
An bukaci Tinubu ya fadi gaskiya kan tallafin mai. Hoto: Bode George|Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Asali: Facebook

Jaridar Punch ta ruwaito cewa dan siyasar ya ce akwai buƙatar gwamnatin Tinubu ta tsage gaskiya ga yan Najeriya kan lamarin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"'Tinubu ya dawo da tallafin mai" - Atiku

Daga cikin abubuwan da suka rikita al'umma akwai yawan cewa gwamnatin Tinubu ta dawo da tallafin man fetur ta bayan fage.

Legit ta ruwaito cewa tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar na cikin waɗanda suka zargi gwamnatin da dawo da tallafin mai a ɓoye.

Bode George ya bukaci Tinubu ya fadi gaskiya

A karkashin haka ne Bode George ya ce ya kamata yan Najeriya su san hakikanin abin da yake faruwa a kan tallafin man fetur.

Vanguard ta wallafa cewa George ya kara da cewa yan Najeriya sun gaji da warwarar zance da gwamnatin tarayya take saboda haka ta fito ta yi magana daya ga yan kasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya feɗewa Tinubu gaskiya, ya faɗa masa halin da ya jefa ƴan Najeriya

Maganar sayar da danyen mai ga Dangote

Bode George ya caccaki gwamnatin tarayya kan shirin sayar da danyen mai ga matatar Dangote da Naira.

George ya ce hakan kuskure ne kuma zai durƙusa tattalin Najeriya wajen rashin samun dala a asusun wajenta.

Tinubu zai kawo motocin CNG Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin tarayya ta kara motsawa domin ganin ta magance radadin cire tallafin fetur da ya jefa talakawa cikin wahalar rayuwa.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da shugaban kamfanin motocin Innoson domin samar da motocin CNG a titunan Najeriya.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng