Rundunar Sojin Najeriya Ta Dauki Matakin Gaggawa Kan Cin Zarafin Farar Hula a Legas

Rundunar Sojin Najeriya Ta Dauki Matakin Gaggawa Kan Cin Zarafin Farar Hula a Legas

  • Rundunar sojin Najeriya ta fusata biyo bayan zargin cin mutunci da jami'anta suka yiwa fararen hula a wata makaranta a jihar Legas
  • Hafsun sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya ba da umurnin ɗaukan matakin kamar yadda rahotanni suka nuna
  • Kungiyar manyan ma'aikatan gwamnati ta kasa (ASCSN) ce ta shigar da korafi biyo bayan zargin jami'an soji da aikata ba daidai ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Lagos - Rundunar sojin Najeriya ta ba da umurnin gaggawa domin yin bincike kan zargin jami'anta da muzgunawa fararen hula.

Hafsun sojojin ƙasan Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ne ya ba da umurnin tare da kira a yi adalci a ciki.

Kara karanta wannan

Sojojin Najeriya sun kashe shugabannin yan ta'adda bayan fafatawa

Sojojin Najeriya
Za a binciki sojojin da suka ci zarafin fararen hula a Legas. Hoto: HQ Nigerian Army
Asali: Facebook

Legit ta gano haka ne cikin wani sako da jami'in yada labaran rundunar ya wallafa a shafinta na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kungiyar ASCSN ta yi korafin sojoji

Kungiyar manya ma'aikatan gwamnati ta kasa (ASCSN) ta shigar da korafi ga rundunar sojin Najeriya bisa zargin cin zarafin ma'aikata.

ASCSN ta ce jami'an soji sun ci zarafin ma'aikata a makarantar sojoji da ke Iyana Ipaja a jihar Legas.

Rundunar soji za ta yi bincike

Biyo bayan korafin, Hafsun sojojin ƙasa, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya umurci shugaban makarantar ya gaggauta yin bincike kan lamarin.

Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya ce bincike zai gano gaskiya tare da lura da korafin da kungiyar ASCSN ta shigar.

"Haka ba zai kara faruwa ba" - Sojoji

Rundunar sojin Najeriya ta ce ma'aikatan da ba sojoji ba suna taka muhimmiyar rawa a harkar gudanar da makarantar.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun wanke jarumar fina finai daga zargin satar zinari, an gano dalili

Saboda haka ta ce za a yi binciken ne domin daukan matakin da zai hana sake faruwar cin zarafin wani ma'aikaci da ba soja ba.

Sojoji sun gargadi Sunday Igboho

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar sojin Najeriya ta gargadi Sunday Adeyemo kan irin kalaman da ya ke yi tun bayan dawowa Najeriya.

Rahotanni sun nuna cewa rundunar ta ce idan har abin da ya fada zai inganta tsaron kasar babu matsala amma sabanin haka kuma ya kauce layi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng