'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 20 a Gari Guda a Jihar Zamfara

'Yan Bindiga Sun Kashe Mutane 20 a Gari Guda a Jihar Zamfara

  • Ƴan bindiga sun buɗe wa mutane wuta a kauyen Bilbis da ke jihar Zamfara, sun kashe maza da mata da ƙananan yara
  • Rahotanni sun bayyana cewa da safiyar ranar Jumu'a aka yi wa waɗanda suka mutu a harin jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada
  • Mazauna yankin sun bayyana cewa ƴan bindigar kewaye su suka yi yayin harin, sannan suka shiga gida-gida daga baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Zamfara - Miyagun ƴan bindigan daji sun halaka "aƙalla mutum 20" da suka ƙunshi magidanta maza da mata da ƙananan yara a kauyen Bilbis da ke jihar Zamfara.

Yayin wannan mummunan harin, ƴan ta'addan sun jikkata wasu mutum bakwai waɗanda yanzu haka suke kwance suna jinya a asibiti.

Kara karanta wannan

"Zamu ceto su," Gwamna Ododo ya mayar da martani kan sace ɗaliban jami'a a Kogi

Gwamna Dauda Lawal na Zamfara.
Yan bindiga sun hallaka maza da mata da kananan yara a Zamfara Hoto: Dauda Lawal
Asali: Facebook

Zamfara: Ta'adin 'yan bindiga a Bilbis

Wani mazaunin kauyen wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda tsaro ya shaidawa jaridar Premium Times cewa:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Sun shigo a kan babura suka kewaye kauyen gaba ɗaya, suka kulle hanyar shiga da ta fita daga garin, sun zo da cikakken shiri."

Ya ƙara da cewa ƴan bindigar ba su yi yunƙurin garkuwa da ko mutum ɗaya ba domin daga zuwa suka buɗe wuta kan mai uwa da wabi.

Ƴan bindiga sun shiga gidaje a Zamfara

Ya ce wasu daga cikin waɗanda aka kashe sun ruga ne da nufin neman tsira amma maharan suka bindige su yayin da wasu kuma har gida suka shiga suka kashe su.

"Galibin matan da aka kashe har gida suka bi suka kashe su saboda idan har aka kawo mana hari, maza ne kaɗai ke guduwa zuwa cikin jeji. Bayan sun halaka wasu mazan, sai suka shiga gida-gida," in ji shi.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun yi artabu da ƴan bindiga a ƙauyuka 2, sun ceto mutane da yawa a Katsina

Lawal Bilbis, wani mazaunin yankin na daban, ya ce al’amuran tsaro sun tabarbare a yankin saboda “kowa ya kama bakinsa ya yi shiru."

An yi wa mamatan jana'iza a Zamfara

An tattaro cewa tuni aka yi wa waɗanda suka rasa rayukansu a harin jana'iza kamar yadda addinin Musulunci ya tanada ranar Jumu'a.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, Yazid Abubakar, bai amsa sakon tes da aka tura masa ba yayin da wayarsa ba ta shiga.

Hare-haren da ake kaiwa a jihar Zamfara musamman a yankunan Tsafe, Zurmi, Maradun, Anka da Bungudu sun karu a 'yan makonnin nan, rahoton Vanguard.

Yan sanda sun ceto mutane a Katsina

A wani rahoton na daban Jami'an ƴan sanda sun daƙile yunƙurin ƴan bindiga na yin garkuwa da mutane tare da kubutar da mutane 13 a jihar Katsina.

Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan jihar, ASP Abubakar Sadiq, ya ce an samu wannan nasara ne a kauyukan Gidan Maga da Unguwar Boka.

Asali: Legit.ng

Online view pixel