Najeriya Na Bin Nijar, Benin, Togo Bashin N5.8bn Na Wutar Lantarki a 2020, Inji Wani Rahoto

Najeriya Na Bin Nijar, Benin, Togo Bashin N5.8bn Na Wutar Lantarki a 2020, Inji Wani Rahoto

  • Yayin da a Najeriya ake ci gaba da kuka game da basussukan da ake bin kasar, ashe kasar na da kudade a wasu kasashen
  • Bangaren wutar lantarki, gwamnatin Najeriya na bi jamhuriyar Nijar, Benin da Togo makudan kudade da har yanzu basu biya ba
  • Najeriya na fama da karancin wutar lantarki, duk da haka kasar na iya raba wutar lantarki da kasashen makwabta

ABIN LURA: Za ku iya ceton rayuwar diya mace dake cikin hadari. Bada gudunmuwarka ga Patreon na Legit

FCT, Abuja - Najeriya na bin jamhuriyar Nijar, Benin da Togo kudaden da suka kai Naira biliyan 5.86 a shekarar 2020 na wutar lantarki da gwamnatin Najeriya ta nemi kasashen su biya.

A rahoton da Daily Trust ta fitar, an ce Najeriya a harkallar wutar lantarki da kasashen, ta nemi su biyu N16.31bn na wutar da ta ba su a shekarar ta 2023.

Kara karanta wannan

Assha: Darajar Naira ta sake raguwa a kasuwar hada-hadar canjin kudade

Rahoto ya nuna adadin kudin wuta da Najeriya ke bin kasashen waje
Najeriya na bin Nijar, Benin, Togo bashin N5.8bn na wutar lantarki a shekarar 2020, inji wani rahoto | Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Kamfanonin kasashen waje da Najeriya ke bi kudaden wutar lantarki

Rahoton na 2020 ya hukumar kula da wutar lantarkin Najeriya (NERC) ta fitar, an bayyana kafamonin kasashen guda uku da ke alhakin biyan wadannan kudaden kamar haka:

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

  1. Societe Nigerienne d’electricite (SNE)
  2. Societe Beninoise d’Energie Electrique (SBEE)
  3. Compagnie Energie Electrique du Togo (CEET)

A cewar Hukumar Kasuwanci ta Najeriya (MO) ana bin kasashen N16.31bn, kuma sun biya N10.45bn yayin da N5.86bn ya rage har yanzu kusan shekaru biyu basu biya ba.

A bangare guda, kamfanin karafa na Ajaokuta ne mafi amfani da wutar lantarki a Najeriya, kuma al’ummar da ke zagaye da kamfanin an ce ba su biya ko anini ba duk da kuwa sun sha wutar akalla N1.08bn a shekarar.

Takardar biyan kudi da kamfanin raba wuta na NBET ya ba kamfanin karafa na Ajaokuta ya kai N930m, yayin da na MO kuwa ya kai wa kamfanin takardar wuta ta N150m.

Kara karanta wannan

Buhari Ya Nada Dangote Wata Mukami Mai Muhammanci a Najeriya

NERC, a cikin rahoton ta ba da shawarar hada kai da MO domin samar da hanyoyin da za su tabbatar da karbar kudaden wuta, musamman a kamfanoni cikin sauki.

Bugu da kari, NERC ta samar da lasisin zamani tare da sabunta na baya da ka iya samar da wutar da ta kai akalla megawatts 667.70.

Sabon lasisin zai iyakara wutar lantarki da megawatts 235 yayin da wanda aka sabunta kuwa zai ba da sama da megawatts 346 na samar da wutar lantarki.

Hakazalika, NERC ya ba da amince kamfanoni 33 tare da ba da lasisi ga wasu 17.

Adadin mitocin wuta da aka raba a Najeriya

Game da batun adadin mitoci da aka raba, rahoton ya nuna cewa an ba da mitoci 537,400 ga jama'a a 2020 kadai, fiye da 60.4% na mitoci 334,896 da aka raba a 2019.

Har yanzu dai, akwai kalubale mai yawa ga kamfanin wura game da rarraba mitar wuta a Naeriya, duba da adadin mutanen da ya kamata a malakawa.

Kara karanta wannan

An kuma: Tururuwa ta cinye takardun kudaden da aka kashe a asusun inshora na NSITF

Adadin masu amfani da wutar lantarki a cewar rahoton ya kara yawa zuwa 11 11,841,819 a 2020, kuma kasa da kwastomomi 4,666,191 ne ke amfani da mita, wanda ke wakilatar 39.40% na adadin masu amfani da wuta.

TCN Ta Roki Ma’aikatan Wutar Lantarki Su Hakura, Kada Su Shiga Yajin Aiki

A wani labarin, kamfanin wutar lantarki na Najeriya (TCN), ya yi kira ga ma’aikatan wutar lantarki da su dakatar da yunkurin yajin aikin da suke shirin farawa a ranar 17 ga watan Agusta, Daily Nigerian ta ruwaito.

Manajan Daraktan TCN, Dokta Sule Abdulaziz ne ya yi wannan roko a cikin wata wasika da ya aike wa ma’aikatan a ranar Talata, biyo bayan barazanar da suka yi na shiga yajin aikin domin warware bukatunsu.

Ma’aikatan da ke karkashin kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa (NUEE), a ranar 15 ga watan Agusta, sun umurci mambobinsu da su mamaye ofisoshin TCN a fadin kasar a ranar 16 ga watan Agusta, daga nan kuma za su fara yajin aiki a ranar 17 ga watan Agusta.

Kara karanta wannan

Ubangiji Yana Amfani da Buhari ne Wurin Ladabtar da 'Yan Najeriya, Yemi Forounbi

Asali: Legit.ng

Online view pixel