Najeriya Zata fara Siyar Da Wutan Lantarki Ga Kasashe Hudu

Najeriya Zata fara Siyar Da Wutan Lantarki Ga Kasashe Hudu

-Najeriya Ta fara Tattauna wa da Kasashe Hudu akan Zata Sayar Musu da Wutan Lantarki da bata Amfani dashi

-Mukaddashin Kamfani Sule Ahmad Abdulaziz,Ya bayyana Haka a wani Taro Daya Gudana a Ranar Laraba akan Batun

-"Lantarkin da ake kokarin saida wa ba mai Amfani ba ce ga Nijeriya"inji shi

Mukaddashi Manajan Daraktan Kamfanin Sadarwar na Nijeriya (TCN) kuma Shugaban Hukumar Gudanarwar Wutar Afirka ta Yamma (WAPP), Engr. Sule Ahmed Abdulaziz, ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin taron WAPP kan aikin Northcore a Abuja.

Jaridar Daily Trust ta Ruwaito cewa kimanin megawatt 2,000 (MW) na wutar lantarki ne Aka ce ba za a iya yin Amfani da shi ba a kowace fadin Kamfanonin Generation (GenCos) a Najeriya Sai dai za a iya fitarwa Zuwa kasashen waje.

Yace:

“Wutan Lantarkin da Zamu sayar Wuta ne da ba a bukata a Najeriya.Wadannan Janaretoci zasu bada wuta ga wannan layin Samar Da Wutan,inda zasu samar da wannan wutar ne Musamman domin wannan aikin. Don haka ta kasance Wuta wanda ba a amfani da shi, ”

Ya kuma kara bayyana cewa Nijeriya na tsammanin Sabbin janareto Wanda Zasu yi Amfani Wurin fitar da makamashin don layin dogo ne Mai kimanin tsawon kilomita 875 kilomita 330 Northcore daga Najeriya zuwa Nijar, Togo, Benin zuwa Burkina Faso.

Bugu da kari, akwai wasu al'ummomin da ke karkashin layin, kusan 611 daga cikinsu wadanda za su samu lantarkin ta yadda ba zai zama wutan ya tsallakesu batare da Sun Samu tagomashi ba. "

KU KARANTA: Nan da watan Yuli zamu fara ginin layin dogon Kaduna zuwa Kano, Minista Amaechi

Najeriya Zata fara Siyar Da Wutan Lantarki Ga Kasashe Hudu
Najeriya Zata fara Siyar Da Wutan Lantarki Ga Kasashe Hudu
Asali: Twitter

KU DUBA: Gwamnatin Amurka ta bukaci a gaggauta dawo da Tuwita Najeriya

Abdulaziz ya ce aikin wanda bankin duniya, majalisar ci gaban Faransa da kuma bankin raya kasashen Afirka suka samar, ya samu ci gaba kuma Ministocin Wutan Lantarki za su magance matsalolin tsaro akan aikin a taron da za su yi a Abuja ranar Alhamis.

Dangane da fa'idodin, shugaban WAPP ya ce,

“Najeriya na da babbar fa'ida a tsakanin waɗannan ƙasashe saboda za a fitar da wutar daga GenCos na Nijeriya.
A dalilin haka, za a inganta kudaden shiga a inda mutane da Dama za su samu aiki a Najeriya. ”

Sakatare-janar na WAPP, Siengui Appolinaire Ki, ya ce:

"Kudin sun kai kimanin dala miliyan 570 kuma wani bangare na saka hannun jari a kowace kasa, ne ta dauki nauyin Sannan masu tallafi suka tallafa musu, kuma Najeriya Zata karbi nata."

Ya kuma ce yarjejeniyar kudade Ya Kammalu yayin da suke jiran fitarwa.

A bangare guda, kamfanin Sunrise Power Transmission Company of Nigeria Ltd watau SPTCL ya na yunkurin kawo cikas a aikin samar da wutar lantarkin Mambilla.

Daily Trust ta ce kamfanin ya shirya kai karar gwamnatin tarayya ya na neman a biya shi $400m ya rage zafi saboda an sabawa yarjejeniyar da aka yi da shi.

Kamar yadda takardun shigar da karar suka bayyana, wannan kamfanin ya dumfari babban kotun kasuwancin Duniya da ke birnin Faris, kasar Faransa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel