Najeriya ta na ba makwabta wuta ne da yarjejeniyar ba za a gina dam a kogin Neja ba

Najeriya ta na ba makwabta wuta ne da yarjejeniyar ba za a gina dam a kogin Neja ba

Mai girma shugaban Najeriya, ya bayyana dalilin da ya sa kasar ta shiga yarjejeniyar fitar da wutar lantarki zuwa kasashen jamhuriyyar Nija, Benin da kasar Togo

Fadar shugaban kasar Najeriya ta ce ta na ba wadannan kasashe wutar lantarki ne da nufin cewa ba za su gina wani dam a yankin kogin Neja wanda kasar ta dogara da shi ba.

Najeriya ta ce adadin kudin da ta ke bin kasar Nijar bashi bai wuce fam Dala miliyan 16 ba, inda kuma ta ke bin kasar Benin bashin fam Dala miliyan hudu a halin yanzu.

Jaridar Vanguard ta rahoto cewa wutar lantarkin da Najeriya ta samar tsakanin 2018 zuwa 2019 ya kai kusan Naira tiriliyan 1.2 watau Dala biliyan hudu.

Wannan bayani ya fito ne bayan wata jarida ta fito ta na cewa gwamnatin tarayya ta fitar da wutar lantarkin $1.2b a kan bashi a lokacin da ake zama cikin duhu a gida.

Wannan jawabi na martani ya fito ne ranar Talata, 28 ga watan Yuli, daga ofishin mai magana da yawun shugaban Najeriya, Malam Garba Shehu.

KU KARANTA: An dakatar da batun kara farashin shan lantarki

Najeriya ta na ba makwabta wuta ne da yarjejeniyar ba za a gina dam a kogin Neja ba
Muhammadu Buhari Hoto: Fadar Shugaban kasa
Asali: UGC

Garba Shehu ya yi tir da wannan rahoto da ya ce karya ta cika shi. Ya ce: “Zuzuta lamari ya cika tunani da aikin wadanda mutane su ke kallo da yarda da amana da gaskiya.”

Shehu ya ce rahoton zai iya ruda mutane. “Bayan cewa adadin da aka fada ko kadan ba kusa da daidai ba ne, tsohon labari ne kuma wanda ba ya bayyana halin da mu ke ciki.”

Hadimin shugaban kasar ya ke cewa wutan da Najeriya ta saida sam ba zai zo daidai da abin da rahoton jaridar ya fada ba.

“An raba sannan an shanye fiye da kashi 90% na wutan da aka samar a Najeriya ne ga kamfanonin raba wuta 11 na kasar.” Inji Shehu wanda ya nemi ‘yan jarida su rika bincike.

“Gwamnatin Najeriya ta na saida wuta zuwa Nija, Benin da Togo ne da yardar cewa ba za su datse ruwan da ke ba mu wuta a Kainji, Shiroro da Jebba ba."

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel