Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar da Duka Jiragen Kamfanin Dana Air Daga Aiki

Gwamnatin Najeriya Ta Dakatar da Duka Jiragen Kamfanin Dana Air Daga Aiki

  • Ministan harkokin sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ba da umarnin dakatar da ayyukan dukkanin jiragen Dana Air
  • Wannan dakatarwar ta biyo bayan iftila'in da ya faru a ranar 23 ga watan Afrilu inda jirgin Dana Air ya kwace a filin jiragen Legas
  • Sanarwar da ma'aikatar sufurin jiragen sama ta fitar ya nuna cewa za a binciki kamfanin domin gano musabbabin faruwar lamarin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya NCAA, ta dakatar da ayyukan kamfanin jiragen sama na Dana Air.

Ministan sufurin jiragen sama, Festus Keyamo ya ba da umarnin dakatarwar saboda damuwar da ke tattare da tsaro da kudaden ayyukan kamfanin.

Kara karanta wannan

Rundunar Najeriya ta kori sojojin da aka samu da sata a matatar Dangote

Gwamnati ta dauki mataki kan Dana Air bayan kwacewar jirgi a Legas
Gwamnatin Najeriya ta dakatar da ayyukan jiragen kamfanin Dana Air, za ta yi bincike. Hoto: @DanaAir
Asali: Facebook

Rahoton jaridar TheCable ya danganta umarnin da lamarin da ya shafi kwacewar jirgin Dana Air a filin jirgin sama na Legas a ranar 23 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnati ta dakatar da jirgin Dana Air

A cewar sanarwar ma'aikatar sufurin jiragen sama mai dauke da sa hannun babban sakatarenta na din-din-din, Dr. Emmanuel Meribole:

"Ministan harkokin sufurin jiragen sama ya karfi korafe-korafe kan abubuwan da suka faru a kwanan nan da kamfanin Dana Airline a filin jiragen sama na Legas.
"Lamarin ya haifar da babbar damuwa da kuma sanya wa mutane shakku game da tsaro da kuma kudaden tafiyar da ayyukan kamfanin.
“Bisa la’akari da muhimmancin kare lafiyar ‘yan kasa da matafiya, ministan ya ba da umarnin a gaggauta dakatar da jiragen na Dana Air har sai an gudanar da cikakken bincike."

Wannan binciken zai shafi dukkanin bangarorin ka'idojin tsaro ga matafiya da ma'aikata da karfin kuɗaden gudanarwa in ji rahoton jaridar Tribune Online.

Kara karanta wannan

Farin ciki a jihar Arewa yayin da farashin shinkafa ya karye daga N60, 000

Jirgin Dana Air ya kwace a Legas

Tun da fari, Legit ta ruwaito wani jirgin sama mallakin kamfanin Dana Air mai lamba Md-82 ya gamu da matsala a Legas bayan tasowa daga Abuja dauke da fasinjoji 83 da ma'aikata shida

An ruwaito jirgin ya kwace bayan sauka a kan titin jirgin sama mai lamba 18L na Murtala Muhammad inda ya fada cikin wani yanki mai ciyayi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel