Matsaloli 6 da rashin shan isashen ruwa ke haifarwa jikin mutum

Matsaloli 6 da rashin shan isashen ruwa ke haifarwa jikin mutum

- Idan aka rasa ruwa, mutum, dabbobi, tsirrai da sauran wasu halittu masu yawa zasu mutu

- Dukkan halittun jikin mutum na bukatar ruwa domin gudanar da aikinsu yadda ya kamata

- Masana sun gano cewa yawan shan ruwa ya fi zama alheri ga jikin mutum a kan karancin shan ruwa

Babu jayayya ko tantama a kan muhimmanci da amfanin ruwa a wurin mutane da dabbobi. Idan babu ruwa, mutum ba zai rayuwa ba.

Karancin ruwa kan kassara lafiyar jikin mutum, hakazalika, rashin shan isashen ruwa yana haifarwa da jiki matsaloli.

Wani binciken kimiyya ya gano cewa masu yawan shan ruwa sun fi koshin lafiya a kan marasa shan isashen ruwa.

Domin gujewa karancin ruwa a jiki (Dehydration) ana so baligin mutum ya sha ruwa akalla kofi takwas a kowacce rana.

KARANTA: Gwamnati ta lissafa muhimman wurare 22 da mabarnata suka lalata

Ruwa yana da muhimmanci ga halittun jikin mutum, yana jika makoshi da taimakawa wajen narka abinci a tumbin mutum.

Matsaloli 6 da rashin shan isashen ruwa ke haifarwa jikin mutum
Matsaloli 6 da rashin shan isashen ruwa ke haifarwa jikin mutum
Asali: UGC

Dukkan halittun jikin mutum na bukatar ruwa domin yin aikinsu yadda ya kamata. Me zai faru kenan idan mutum ba ya shan isashen ruwa? Legit.ng Hausa ta ci karo da amsar wannan tambaya a wani rahoto da The Nation ta wallafa.

1. Rashin kuzari

Idan ruwa ya yi karanci, ko yawansa ya ragu sosai, a jiki, mutum zai ji kasala da rashin kuzari. Mutum zai ji ya gaza cigaba da aikinsa.

KARANTA: Sai murna: FG ta sanar da fara biyan N30,000 ga masu sana'ar hannu 300,000 a jihohi 11

2. Hatsarin kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki

A wani binciki da aka yi a wata cibiyar cututtukan zuciya (BMC Cardiovascular Disorders), an gano cewa karancin ruwa na saka jiki a hatsarin kamuwa da cutar mutuwar rabin jiki tare hana warkewa da wuri idan cutar ta samu mutum.

3. Rashin saurin narkewar abinci a ciki

Abincin ba ya saurin narkewa a cikin yayin da mutum ke jin kishin ruwa ko kuma idan babu isashen ruwa a jikinsa.

4. Ciwon kai

Saboda kwakwalwa tana bukatar ruwa, duk lokacin da ya kasance babu wadatarsa a jikin mutum, sai ya ji gajiya da ciwon kai.

5. Rashin kyan fatar jiki

Fatar jikin mutum ta na bukatar ruwa kafin ta kasance cikin yanayi mai kyau. A saboda haka, rashin shan isashen ruwa zai sa fatar mutum ta ke bushewa, lamarin da ke saurin tsofar da fata.

6. Kiba

Yawan shan ruwa zai iya taimakawa jiki wajen rage teba. Rashin shan isashen ruwa zai iya sa mutum ya kara kiba.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng