'Yan Majalisar YPP 2 da Aka Dakatar Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Labour

'Yan Majalisar YPP 2 da Aka Dakatar Sun Sauya Sheka Zuwa Jam'iyyar Labour

  • 'Yan majalisar dokokin jihar Abia, Hon. Iheanacho Nwogu da Hon. Fyne Ahuama sun sauya sheka daga jam'iyyar YPP zuwa Labour
  • Kakakin majalisar jihar, Rt. Hon. Emmanuel Emeruwa ya karanta wasikunsu na sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour a yau Talata
  • Nwogu da Ahuama sun yi alkawarin marawa gwamnatin Alex Otti baya tare da yakinin cewa jam'iyyar LP ta kafu kan adalci

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Abia - Mambobi biyu na jam’iyyar Young Progressive Party (YPP) a majalisar dokokin jihar Abia sun fice daga jam’iyyar zuwa jam’iyyar Labour Party (LP).

'Yan majalisar YPP sun sauye sheka zuwa jam'iyyar LP a Abia
Abia: 'Yan majalisar jam'iyyar YPP 2 sun sauya sheka zuwa Labour. Hoto: Iroegbulam
Asali: Facebook

‘Yan majalisar daga karamar hukumar Osisioma ta jihar, su ne: Hon. Iheanacho Nwogu daga Osisioma ta Arewa da Hon. Fyne Ahuama daga Osisioma ta Kudu.

Kara karanta wannan

Dalibai 14 cikin 24 da aka sace a jami'ar Kogi sun kubuta, 'yan sanda sun yi bayani

YPP - LP: Dalilin sauya shekarar 'yan majalisar

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa ba a jima ba YPP ta dakatar da ‘yan majalisar saboda wasu ayyukan da suka saba wa jam’iyyar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugaban majalisar jihar, Rt. Hon. Emmanuel Emeruwa ya karanta wasikunsu na sauya sheka zuwa jam’iyyar Labour a yau Talata, 14 ga watan Mayu.

'Yan majalisa sun bar YPP, sun bi Otti

A cikin bayanin nasu, Hon Nwogu da Hon Ahuama sun yi alkawarin marawa gwamnatin Alex Otti baya tare da yakinin cewa "jam'iyyar Labour ta kafu kan tsarin adalci."

An ga Hon. Hon. Fyne Ahuama ya wallafa hoton jam'iyyar Labour a shafinsa na Facebook tare da yin rubutun da ke nuna shigarsa jam'iyyar.

'Yan kwadago sun rufe hedikwatar NERC

A wani labarin, mun ruwaito cewa kungiyoyin kwadago na kasa sun rufe hedikwatar hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC).

Kara karanta wannan

Zargin rusa gidajen 'yan majalisa: Magoya bayan Wike sun fita zanga zanga a Port Harcourt

Wannan na zuwa ne yayin da 'yan kwadagon suka mamaye ofisoshin kamfanonin rarraba wutar lantarki na jihohi bayan hukumar ta gaza janye karin kudin wutar da ta yi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.