Dala a Babbar Riga: Hadimin Atiku Ya Dage, Yana So Hukumar EFCC Ta Binciki Ganduje

Dala a Babbar Riga: Hadimin Atiku Ya Dage, Yana So Hukumar EFCC Ta Binciki Ganduje

  • Demola Rewaju yana so jami’an EFCC su maida hankali wajen binciken tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje
  • Idan EFCC da gaske take yi wajen yakar rashin gaskiya, ya ce ta cafke Ganduje yadda aka kamo Cubana kwanakin baya
  • A cewar Demola Rewaju, akwai bidiyo da za su iya daure shugaban na APC yadda EFCC ta damke fitaccen ‘dan kasuwar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Lagos - Demola Rewaju matashin ‘dan siyasa ne kuma ‘dan ga ni-kashe nin jam’iyyar PDP, ya yi kira ga hukumar EFCC ta kasa.

A yayin da yake tofa albarkacin bakinsa a dandalin X da aka fi sani da Twitter, ya bukaci a binciki Abdullahi Umar Ganduje.

Ganduje da EFCC
Ana so Hukumar EFCC ta waiwayi Abdullahi Ganduje Hoto: @OfficialEFCC, @Dawisu
Asali: Twitter

'Bidiyon' Dala: EFCC da Abdullahi Ganduje

Kara karanta wannan

Gwamna Ododo ya hana a cafke Yahaya Bello? Gaskiya ta bayyana

Demola Rewaju yana ganin idan da gaske ake so a yaki cin hanci da rashawa, ya zama dole a kama tsohon gwamnan Kano.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A lokacin yana gwamna, an zargi Abdullahi Umar Ganduje da yawan karbar rashawa daga hannun ‘yan kwangila a jihar Kano.

Duk da jerin faya-fayen bidiyo da aka rika bankadowa a lokacin, ba a ji hukumar EFCC ta binciki Ganduje bayan barin ofis ba.

Ganduje: Kiran Demola Rewaju ga EFCC

"Idan da gaske take yi, ya kamata a ce tana taimakawa gwamnatin Kano wajen cafke shugaban APC, Abdullahi Ganduje kuma a gurfanar da shi."
"Hujjojin bidiyon Cubana yana jefa kudi daidai yake da hujjojin bidiyon Ganduje yana cusa daloli a cikin babbar riga."

- Demola Rewaju

EFCC za ta bi Ganduje kamar Cubana, Bobrisky?

Hadimin na Atiku Abubakar ya ce EFCC ta rabu da irinsu Cubana da Bobrisky, ta daina wata-wata, ta kama Dr. Abdullahi Ganduje.

Kara karanta wannan

Yahaya Bello: Hukumar NIS ta umarci jami'ai su sanya ido kan motsin tsohon gwamna

‘Dan siyasar ya kawo misali da yadda EFCC ta tuhumi shugaban jam’iyyar PDP na kasa Tafa Balogun da laifi lokacin mulkin PDP.

Kamar yadda ya nuna a shafinsa, idan aka bi ta tashi, za a binciki Akinwumi Ambode.

"Idan a lokacin PDP, EFCC za ta iya kama shugaban jam’iyya kuma har a je kotu da Sufetan ‘yan sanda, EFCC a zamanin APC ta shirya yin abin da ya dace ga Najeriya."

- Demola Rewaju

Zargin cin hanci da rashawa a kwastam

Kwanaki kun ji labarin ana zargin wani jami’in kwastam ya soke cin hancin N1.1bn, an gano $31, 200 da N500, 000 a hannunsa

Binciken hukumar EFCC ya nuna akwai wani jami'i wanda ake zargin an ba cin hancin kusan N10bn a shekaru takwas.

Akwai hadimin wani babban ma’aikacin da ya maidowa EFCC N12m a cikin N126m da ake zargin ya wawura ta hanyar ofishinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel