Yahaya Bello: Hukumar NIS ta Umarci Jami'ai su Sanya Ido Kan Motsin Tsohon Gwamna

Yahaya Bello: Hukumar NIS ta Umarci Jami'ai su Sanya Ido Kan Motsin Tsohon Gwamna

  • Hukumar NIS ta umarci jami'anta da cafke tsohon gwamnan Kogi Yahaya Bello a duk inda suka gan shi yana kokarin ficewa daga kasar
  • Wanna ya biyo tuhumar da EFCC take masa na karkatar da miliyoyin kudi daga baitul malin gwamnati
  • Ana zargin Yahaya Bello da wasu mutane uku da almundahanar kudin jama'a sama da naira miliyan 80

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Abuja- Hukumar shige da fice ta Najeriya(NIS) ta sanya tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello cikin wadanda take sanyawa idanu.

Wanna na zuwa bayan rundunar 'yan sandan kasar nan ta janye jami'in jami'anta da ke tsaron tsohon Gwamnan.

Kara karanta wannan

Baɗaƙalar N80bn: Gwamnatin Tinubu ta yi magana kan rikicin Yahaya Bello da EFCC

Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya ello
NIS ta umarci jami'anta su cika hannunsu da tsohon gwamnan idan sun gan shi Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Asali: Facebook

A kwanakin nan, Yahaya Bello ya shiga matsala bayan hukumar hana yi wa tattalin arzikin kasa ta'annati (EFCC) ta fara tuhumarsa da laifin karkatar da makudan kudi, kamar yadda TheCable ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

EFCC na zargin Yahaya Bello ya karkatar da naira miliyan 80.2 daga baitul malin jiharsa da taimakon wani Dauda Suleiman.

NIS ta yi umarnin cafke Yahaya Bello

A takardar da mataimakin shugaban hukumar NIS, ACI DS ya sanyawa hannu, an umarci duk jami'an hukumar su cafke Yahaya Bello. idan suka yi ido hudu da shi a iyakokin kasar nan , ko yana kokarin guduwa daga kasar.

Sanarwar da wata mai amfani da shafin X, Debora Tolu-Kolawole GenZ, @DeborahToluwase ta wallafa ta nuna ana zargin binciken tsohon gwamnan kan almundahanar kudi masu tarin yawa

EFCC na zargin Yahaya Bello da almundahana

Kara karanta wannan

Kasar Yarbawa: Kotu ta rufe masu fafutukar raba Najeriya bisa zargin cin amana

A Alhamis din nan ne hukumar EFCC ta bayyana cewa ta kammala shirin gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello gaban kotu, wanda hakan ya jefa shi tsaka mai wuya.

EFCC ta yi kokarin cafke Yahaya Bello a gidansa da ke Abuja na zarginsa da karkatar da kudin jama'ar jiharsa lokacin yana gwamna har Naira miliyan 80.2.

Mai Shari'a Emeka Nwite ne zai saurari tuhumar da ake yi wa Yahaya Bello da wasu mutane uku da suka hada da Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdulsalam Hudu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel