Bayan Kalaman Tinubu, Gwamnan Arewa Ya Ƙara Wa Ma'aikata Albashi a Watan Azumin Ramadan

Bayan Kalaman Tinubu, Gwamnan Arewa Ya Ƙara Wa Ma'aikata Albashi a Watan Azumin Ramadan

  • Awanni bayan kalaman Bola Ahmed Tinubu, Gwamna Umar Bago ya amince da biyan N20,000 a matsayin kyautar albashi ga ma'aikatan jihar Neja
  • Yayin ziyarar da ya kai Minna, Shugaba Tinubu ya roki gwamnoni su fara biyan kyautar albashi domin rage raɗaɗin da mutane ke ciki
  • Bayan ƙarin albashin, Gwamna Bago ya ce gwamnatinsa za ta raba tirolin hatsi kyauta da kuma ciyar da talakawa a watan Ramadan

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Gwamna Muhammad Umar Bago na jihar Neja ya amince da biyan tallafin albashi na 20,000 ga dukkan ma'aikatan gwamnatin jihar.

Wannan ƙarin albashi na wucin gadi da Gwamna Bago ya yi ya zo ne bayan shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya roƙi gwamnoni su aiwatar da tsarin kyautar albashi.

Kara karanta wannan

Ramadan: Shugaba Tinubu ya halarci buɗe tafseer na alƙur'ani, ya aika saƙo ga Musulmin Najeriya

Gwamna Umar Bago na jihar Neja.
Ma'aikatan jihar Neja za su fara jin alat na ƙarin albashi ranar Laraba Hoto: Muhammad Umar Bago
Asali: Twitter

Menene manufar ƙarin albashin wucin gadi?

Shugaba Tinubu ya ce ɗan ƙarin da ma'aikatan za su samu a albashinsu na wata-wata zai taimaka wajen rage tasirin matsin tattalin arzikin da jama'a ke fuskanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tinubu ya buƙaci gwamnatocin jihohi su fara biyan ƙarin albashin gabanin kammala aiki kan sabon mafi ƙarancin albashi domin rage wa ma'aikata wahala.

Shugaban ƙasar ya yi wannan roko ne yayin da ya kai ziyarar aiki ta kwana ɗaya a Minna, babban birnin jihar Neja ranar Litinin, kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Shugaban ya ja hankalin cewa akwai bukatar gaba ɗaya jihohin kasar nan su amince da kyautar albashin, yana mai cewa majalisar zartaswa ta kasa ma za ta amince da shi.

A rahoton Leadership, Tinubu ya ce:

“Don Allah ba umarni nake ba ku ba, ina rokon jihohi ku fara biyan tallafin albashi ga ma’aikata,

Kara karanta wannan

Remi Tinubu ta yi martani kan barazanar kisan da wani malamin addini ya yi mata

kowa ya yi ƙoƙari ya fara biya, zai rage mutane raɗaɗin halin da suke ciki."

Ramadan: Gwamna Bago ya shirya tallafawa al'ummarsa

Gwamnan jihar Neja ya amince da biyan N20,000 a matsayin tallafin albashi ga ma'aikata a taron majalisar zartarwar jihar da aka gudanar a Minna ranar Laraba.

Gwamna Bago ya bada tabbacin cewa za a fara biyan kudin ba tare da ɓata lokaci ba a ranar Laraba kuma ma’aikata za su fara jin shigowar kudi a wayoyinsu.

Bago ya ce za a ciyar da mutane a wurare daban-daban a watan Ramadan yayin da gwamnatin jihar za ta fara rabon kayan abinci tirela 120 na hatsi domin rage radadin halin da jama’a ke ciki.

Tsaro: Gwamnan PDP ya hango matsala

A wani rahoton kun ji cewa Ademola Adeleke na jihar Osun ya banƙado wani shiri na kai sababbin hare-hare makarantu da gonakin al'umma a kauyukan jihar.

Gwamna Adeleke ya bayyana cewa ya samu bayanan sirri da ke nuna cewa wasu gurɓatattu na shirin kawo cikas a harkar noma da ilimi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel