Budurwa Ta Fada Tarkon Son Direban Bolt da Ta Shiga, Ta Yada Bidiyo

Budurwa Ta Fada Tarkon Son Direban Bolt da Ta Shiga, Ta Yada Bidiyo

  • Wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya ta yi nutso a cikin son direban Bolt sannan ta nunawa duniya shi a soshiyal midiya
  • Ta ce ta fada tarkon sonsa sannan ta dungi nuna sha'awarta ga zanen jikinsa yayin da ta dauke shi bidiyo don mutane su gani
  • Sai dai kuma, sam wannan abu da ta yi bai burge mutane da dama ba yayin da suka gano tangarda a bidiyonta

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata matashiyar budurwa 'yar Najeriya, @jojooflele, ta bayyana cewa ta fada a tarkon son dirabn Bolt dinta.

Da take yada bidiyonta yayin da mai tasi din ke tuka ta, matashiyar ta rikice akan kyawu da zanen jikinsa.

Saurayi da budurwa
Budurwa Ta Fada Tarkon Son Direban Tasi da Ta Shiga, Ta Yada Bidiyo Hoto: @jojooflele
Asali: TikTok
"POV: Na fada tarkon son direban tasi dina kumaina matukar sha'awar zanen jikinsa," taken da ta yiwa bidiyon kenan.

Kara karanta wannan

"Za su illata ni": Matashi ya koka da 'yan Nepa suka bar lantarkin tsawon kwanaki 5 a jere

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sai dai kuma, direban Bolt din bai furta komai ba yayin da matashiyar ke daukarsu bidiyo a tare. Bidiyon @jojooflele ya yadu a soshiyal midiya.

Kalli bidiyon a kasa:

Jama'a sun yi martani akan bidiyon matashiyar

Iamgreat ya ce:

"Ubangijin da mutumin nan ke bautawa zai kare shi daga nisa."

Drey ya ce:

"Mace da neman tsokana... haka za a yi mai tasi ya turmushe budurwar wani."

Ejituru jnr ya ce:

"Duk wanda ka gani da haka kake fadawa tarkon so...kin kusa zama uwa."

Jane babe tace:

"Wannan ne dalilin da yasa bana so mijina ya yi, da zaran ya dawo daga dandalinsa."

Traccy ta ce:

"Ba Victor ba kenan? Matarsa ta haihu kimanin wata daya da ya shige."

iykon ta ce:

"Saurayinki kike kira direban tasi."

Direban Uber ya cinye abincin sako

A wani labarin, wata matashiya yar Najeriya mai suna @ozzyetomi ta je dandalin Twitter domin ba da labarin wani a al'amari mai ban mamaki da ya faru tsakanin wata da direban Uber.

Kara karanta wannan

Bidiyon wani bahaushe da ya yanka kek da wayar iPhone 12 Pro Max ya girgiza intanet

Dirama ya barke bayan kawarta ta tura direban Uber ya karbo mata abincin Sallah daga wajen wata kawarta.

A cewar @ozzyetomi, direban Uber din ya gaggauta kawo karshen tafiyar tasa, sannan ya sace abincikin tare da tura sakon ban hakuri bayan ya cinye abincin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel