“Za Su Illata Ni”: Matashi Ya Koka da Yan Nepa Suka Bar Lantarki Tsawon Kwanaki 5 a Jere

“Za Su Illata Ni”: Matashi Ya Koka da Yan Nepa Suka Bar Lantarki Tsawon Kwanaki 5 a Jere

  • Wani mutumi ya haddasa cece-kuce a soshiyal midiya yayin da ya yi murnar samun wutar lantarki ba tare da tangarda ba a Aba
  • Da yake nuna firinjinsa da ya kankare, mazaunin yankin na Aba ya koka cike da barkwanci cewa "suna so su illata shi da wutar lantarki"
  • Jama'a sun yi martani kan haka yayin da wasu suka caccake shi kan barnatar da wutar lantarkin da suke samu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wani mazaunin Aba ya yi murnar morar wutar lantarki ba tare da tangarda ba a garinsa tsawon kwanaki biyar a jere.

Wani bidiyon mutumin yana murna kan ci gaban cikin yanayi mai ban dariya ya yadu a Instagram bayan @gossipmilltv ya wallafa shi.

Kara karanta wannan

Bidiyon wani bahaushe da ya yanka kek da wayar iPhone 12 Pro Max ya girgiza intanet

Matashi ya yi murnar samun lantarki mai dorewa a Aba
Mutumin ya ce kwanaki biyar kenan rabon da a dauke masu wuta Hoto: @gossipmilltv
Asali: Instagram

Wutar lantarki babu tangarda a Aba

Bidiyon na @gossipmilltv ya haifar da martani a soshiyal midiya. 'Mutumin ya jinjinawa Gwamna Alex Otti na jihar Abia kan inganta wuta a garin nasa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya nuno yadda firinjinsa ya kankare sannan ya fitar da lemun da ke ciki.

Tun lokacin da aka dasa tashar samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 188 a Abia, mazauna yankin suke cikin farin ciki.

Jama'a sun yi martani a kan bidiyon

warriednut ya ce:

"Mutanen da aka ba wuta domin bunkasa tattalin arzikin jihar da janyo masu zuba jari. Gwamnanmu na gina gadar sama. Ban san me yake son janyowa ba."

metro_blog ya ce:

"Da ace muna da shugaban kasa mai kyau shin da firinjin nan ya cika da lemu yanzu."

graceybecky_clothing ta ce:

"Akwai akai-akai yanzu ba kamar da ba...wasu lokutan zan dawo gida na ga wuta har washeagari. Ba awa 24 ba amma mutumin na kokari.

Kara karanta wannan

Daliban jami'a 4 sun lakadawa abokin karatunsu duka har ya mutu, ‘yan sanda sun dauki mataki

dozzybreezy ya ce:

"Ku tayani godiya ga Allah ni d'an jihar Abia ne, gwamnan mu ya fi na kowa."

'Dan Ganduje ya samu mukami

A wani labarin, mun ji cewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da Manajan Darakta/Shugaba na hukumar wutar lantarki ta karkara (REA), Ahmad Salihijo Ahmad.

Bola Tinubu ya dakatar da Ahmed Salihijo tare da wasu daraktoci uku na hukumar har sai baba ta gani.

Asali: Legit.ng

Online view pixel