Kyakkyawar Baturiya Ta Furta Soyayyarta Ga ‘Yan Najeriya, Ta Nemi a Kawo Ta Najeriya a Bidiyo

Kyakkyawar Baturiya Ta Furta Soyayyarta Ga ‘Yan Najeriya, Ta Nemi a Kawo Ta Najeriya a Bidiyo

  • Wata baturiya ta haddasa cece-kuce a tsakanin masu amfani da Twitter bayan ta ayyana soyayyarta ga Najeriya da mutanenta
  • Kyakkyawar baturiyar ta magantu game da irin son da take yi wa Najeriya bayan wani matashi ya aika mata sako cewa yana sonta
  • Jama'a sun bayyana ra'ayoyinsu kan sakonta ga 'yan Najeriya, inda mutane da dama suka jinjina mata saboda yadda ta fito fili ta nuna soyayyarta ga kasar

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Wata baturiya ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta bayyana zuciyarta game da son da take yi wa 'yan Najeriya.

A cikin wani bidiyo na TikTok, @raistii ta yi martani ga wani mutum da ya ce shi 'dan Najeriya ne kuma yana son ta.

Kara karanta wannan

"Ba ta siyarwa bace": Uba ya mayarwa ango da kudin sadakin diyarsa, ya yi magana 1 mai ratsa zuciya

Baturiya mai son 'yan Najeriya
Kyakkyawar Baturiya Ta Furta Soyayyarta Ga ‘Yan Najeriya, Ta Nemo a Kawo Ta Najeriya a Bidiyo Hoto: @raistii
Asali: TikTok

Ga mamakin mutane, @raistii ta amsa masa, cewa bai kamata ace duk mutumin da ya fito daga Najeriya ya so ta ba face dai ya kaunace ta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta ce:

"Ba za ka iya sona ba idan ka fito daga Najeriya ne. Idan kai 'dan Najeriya ne, dole ka kaunace ni saboda ina kaunar Najeriya. Ba ku ga bidiyoyina ba.
"Ka kai ni Najeriya idan kana sona."

Kalli bidiyon a kasa:

Mutane sun mato a kanta

Otisunday Emeka ya ce:

"Ina kaunarki ni 'dan Najeriya ne kuma kina iya zuwa Najeriya.
"Ina mutunta haka."

Vans Evakee ya ce:

"Don Allah ni fa, a bangarena ina matukar kaunarki, daga Ghana."

TKleesky ya ce:

"Toh ina kaunarki kuma ina so mu fara soyayya."

WaleALAYO ya ce:

"Ina kaunarki 'yar mata, kina da abun burgewa."

Kara karanta wannan

"Adaidaita ya kai miliyan 2.6 yanzu": Matashi da ya je shagon adaidaita ya koka saboda tsadarsa

SON OF JATTO ya ce:

"Kina da sa'a.
"Na zata ,a wani abin wawuyar ke fadi."

JAY BOY FF ya ce:

"Kalli yarinyar nan fa tana so ta zo kasar da garin kwaki ya yi tsada."

Jarumar fim ta ce baturiya take son zama

A wani labarin, jarumar fina-finan Kudu wato Nollywood, Destiny Etiko, ta bayyana cewa idan har Allah zai sake halitto ta a wata rayuwar, toh a baturi take so ta zo. '

Jarumar ta bayyana hakan ne yayin da take martani ga wani bidiyo da mai watsa shirye-shirye ta Instagram, Tunde Ednut ya wallafa, inda ya yan mata biyu dake bayani kan yancin cin gashin kansu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel