Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Babban Ministan Tinubu, Bayanai Sun Fito

Majalisar Dattawa Ta Gayyaci Babban Ministan Tinubu, Bayanai Sun Fito

  • Majalisar dattawan Najeriya ta buƙaci samun amsoshi dangane da halin da ake ciki na rashin tsaro a babban birnin tarayya Abuja
  • Majalisar dattawan ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike da kwamishinan ƴan sanda a ranar Laraba
  • Wannan ya biyo bayan hare-hare da sace-sacen mutane a birnin yayin da Wike ya sha alwashin ganin bayan masu aikata laifuka a birnin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Biyo bayan taɓarɓarewar tsaro a Abuja, majalisar dattawa ta gayyaci ministan babban birnin tarayya, Nyesom Wike, da kwamishinan ƴan sandan Abuja domin yiwa majalisar bayani a wani zama na sirri.

Majalisa ta gayyaci Wike
Rashin tsaro a Abuja ya sa majalisa ta gayyaci Wike Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS
Asali: Facebook

Me ya sa majalisar ta gayyaci Wike?

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, za a gudanar da taron ne kan tsaro a babban birnin tarayya Abuja, duba da abin da ya faru na sace-sacen da aka yi a Galadima a ƴan kwanakin nan.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Majalisar dattijawan ta amince da hakan ne bayan wani ƙudiri da Sanata Ned Nwoko, mai wakiltar Delta ta Arewa ya gabatar kan buƙatar gaggauta inganta matakan tsaro a babban birnin tarayya Abuja yayin zaman majalisar a ranar Laraba.

Daga cikin ƙudurorin da majalisar dattawan ta zartas sun haɗa da yin kira ga babban sufeton ƴan sanda, da ya gaggauta ƙara matakan tsaro da sa ido a cikin Abuja da ma ƙasar baki ɗaya, domin yaƙi da satar mutane a faɗin ƙasar nan, inji rahoton Premium Times.

Har ila yau, sun umarci Sufeto-Janar na ƴan sandan da ya ga an sanya na’urorin ɗaukar hoto na CCTV a wurare masu muhimmanci a ciki da wajen Abuja, manyan tituna, da sauran manyan biranen ƙasar nan domin ƙarfafa sa ido da daƙile ayyukan miyagu.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

Ƴan majalisar sun kuma yi shiru na tsawon minti ɗaya domin girmama waɗanda aka kashe sakamakon muguntar waɗannan ƴan bindiga.

Hakan ya biyo bayan da rundunar ƴan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama Samaila Wakili Fafa, wanda ake kira Habu Ibrahim, wani shugaban masu garkuwa da mutane.

Wike Ya Sanya Babbar Kyauta

A wani labarin kuma, kun ji cewa ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya sanya kyauta domin cafko masu garkuwa da mutanen da suka addabi mutanen Abuja.

Ministan ya sanya kyautar N20m domin cafko wasu riƙaƙƙun masu garkuwa da mutane da suka daɗe suna addabar mutanen birnin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel