An Sake Nasarar Cafke Kasurgumin Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Arewa, Ya Fadi Ta'asar da Ya Aikata

An Sake Nasarar Cafke Kasurgumin Dan Bindiga da Ya Addabi Jihar Arewa, Ya Fadi Ta'asar da Ya Aikata

  • Rundunar 'yan sanda a birnin Abuja ta yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta'adda da ya addabi birnin da kewaye
  • Rundunar ta tabbatar da cafke wanda ake zargi ne mai suna Sama'ila Wakili Fafa a dajin Sardauna da ke jihar Nasarawa
  • Kwamishinan rundunar 'yan sanda, Benneth Igweh shi ya bayyana haka a jiya Talata 27 ga watan Faburairu a birnin Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT Abuja - Rundunar 'yan sanda a birnin Tarayya ta cafke wani kasurguman dan ta'adda da ya addabi jihar Nasarawa.

Wanda ake zargin, Sama'ila Wakili Fafa an cafke shi da misalin karfe 7 na yamma a dajin Sardaunan da ke jihar, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

An kama kasurgumin mai garkuwa da mutane da ya addabi babban birnin tarayya Abuja

Yan sanda sun sake cafke wani kasurgumin dan ta'adda
Dan ta'addan bai musanta dukkan abin da ake zarginsa ba. Hoto: NPF.
Asali: Facebook

Yaushe rundunar ta cafke dan ta'addan a Abuja?

Kwamishinan rundunar 'yan sanda, Benneth Igweh shi ya bayyana haka a jiya Talata 27 ga watan Faburairu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Igweh ya ce dan ta'addan na daga cikin kasurguman 'yan ta'adda guda biyu da ake nema ruwa a jallo.

Ya ce an yi nasarar cafke shi ne bayan Ministan Abuja, Nyesom Wike ya sanar da kyautar miliyan 20 ga duk wanda ya nemo su.

A cewarsa:

"Idan ba ku manta dan ta'addan na daga cikin kasurguman 'yan bindigan biyu da Nyesom Wike ya bayar da miliyan 20 don kamo su.
"Yayin da daya daga ciki mai suna Abdulkadir Sa'idu ya shiga hannun 'yan sanda a kwanakin nan."

Wanda ake zargin ya tabbatar da aikata laifukan garkuwa da mutane da dama a Abuja da kewayenta, cewar BusinessDay.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Tarayya za ta fara biyan matasa marasa aikin yi alawus, bayanai sun fito

Daga cikin laifukan akwai garkuwa da Barista Chris Agidy, hadimi a bangaren Shari'a ga Sanata Ned Nwoko.

Har ila yau, shi ne ya sace mai sarautar gargajiya a Ketti, marigayi Mista Sunday Yahaya Zakwai a kwanakin baya.

Wani matashi ya hallaka mahaifinsa

Kun ji cewa Rundunar ‘yan sanda a jihar Plateau ta kama wani matashi mai shekara 29, Joseph Yakubu da zargin kashe mahaifinsa, Yakubu Dalyop.

Rahotanni sun tattaro cewa 'yan sandan sun kama matashin ne bisa zargin ya buga wa mahaifinsa tabarya inda Dattijo ya ce ga garinku.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Online view pixel