'Yan Sanda Za Su Sha Kyautar Miliyoyi Daga Wike, Sun Kamo Dan Bindigan da Ya Addabi Jama’a a Abuja

'Yan Sanda Za Su Sha Kyautar Miliyoyi Daga Wike, Sun Kamo Dan Bindigan da Ya Addabi Jama’a a Abuja

  • ‘Yan sanda a Abuja sun yi nasarar kame wani kasurgumin dan bindigan da ke kitsa kashe-kashe da sace-sace a birnin
  • Ministan Abuja ya sanya lada ga duk wanda ya kamo wasu ‘yan bindigan da suka addabi birnin tarayyar Najeriya
  • Abuja ta zama daga garuruwan da ake yawan samun ayyukan ta’addanci a Najeriya duk da kasancewarta babban birni

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Salisu Ibrahim ne babban editan (Copy Editor) sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - Rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja ta kama wani kasurgumin mai garkuwa da mutane, Sa’idu Abdulkadir.

Wannan na fitowa ne daga bakin kwamishin 'yan sandan birnin, CP Benneth Igwe a lokacin da yake zantawa da manema labarai.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kona mutane 12 har lahira, sun kuma babbake gidaje 17 a wata jihar Arewa

An kama dan bindigan da ya addabi jama'a a Abuja
An kama tsageran da ya addabi jama'a a Abuja | Hoto: Nyesom Ezenwo Wike - CON, GSSRS, NPF
Asali: Facebook

Ya ce sun yi nasarar kamun ne bayan wani samame da suka kai a sansanonin masu garkuwa da mutane da ke kan iyaka da Nasarawa da Abuja ta karamar hukumar Kuje, da tsakar daren ranar Alhamis.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yadda aka buga tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan sanda

A cewarsa, a daidai lokacin da ‘yan bindigar da suka ga jami’an, nan take suka bude wuta kan ‘yan sandan, amma daga karshe aka fi karfinsu.

Hakazalika, ya ce kai samamen ya kai ga kubutar da wasu da aka yi garkuwa dasu, Habu Yakubu da Isufu Abubakar, rahoton Daily Trust.

Da yake bayyana laifukan da suka aikata a baya, Igwe ya bayyana cewa:

“Binciken farko da rundunarmu ta gudanar ya nuna cewa wanda ake zargin shi ne ya kitsa sacewa tare da kashe hakimin gundumar Ketti a AMAC, Mista Sunday Yahaya Zakwai.”

Kara karanta wannan

Wasan karshe na AFCON: Gaskiyar batu kan bidiyon da ke zargin golan Ivory Coast da sanya guraye

Wike ya yi alkawarin ba da miliyoyi ga wadanda suka kama ‘yan bindiga

A cewarsa, kama Adamu babbar nasara ce ga rundunar da kuma gwamnatin babban birnin tarayya Abuja, wanda ya ce hakan zai dawo da zaman lafiya da tsaro a yankin, PM News ta ruwaito.

A tun farko, ministan Abuja, Nyesom Wike ya alanta ba da ladar Naira miliyan 20 kan wasu masu garkuwa da mutane biyu da suka addabi birnin a ranar Litinin.

Wannan yasa Igwe yake yabawa Wike bisa jajircewa da kokarin tabbatar da zaman lafiya a babbar birnin na Najeriya mai cike da ofisoshin gwamnati.

An hallaka jigon APC a Plateau

A wani labarin, kun ji yadda wasu tsageru suka harbe wani jigon jam’iyyar APC a jihar Plateau da ke Arewacin Najeriya.

Wannan na zuwa ne a daidai loakcin da ake ci gaba da kuka yadda aka yi kashe-kashe a wasu yankunan jihar.

A cewar majiya, an kashe jigon an APC ne a lokacin da ya kai ziyarar gaisuwar rasuwa a yankin Pankshin na jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel