Bukatu 20 da NLC Ta Gabatarwa Shugaban Kasa Tinubu Wajen Dakatar da Zanga Zanga

Bukatu 20 da NLC Ta Gabatarwa Shugaban Kasa Tinubu Wajen Dakatar da Zanga Zanga

  • Kungiyar NLC ta ‘yan kwadago da sauran takwarorinta sun dakatar da zanga-zangar lumunar gama-garin da aka shirya
  • Shugabannin ‘yan kwadago sun gabatar da jerin bukatu ga gwamnatin Bola Tinubu wadanda suke so a aiwatar da su
  • NLC tana so gwamnatin tarayya ta cika alkawuran da ta dauka, kuma a fara ganin an aiwatar da duka yarjejeniyar da aka yi

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Abuja - An rahoto ‘yan kwadago sun shafe kwanaki biyu a jere ana zanga-zanga a garuruwa saboda tsada da wahalar rayuwa.

A karshe zanga-zangar ta zo karshe, amma Vanguard ta ce NLC ta gabatar da bukatu ga gwamnatin Bola Tinubu da za a cika mata.

Kara karanta wannan

Masu zanga-zanga sun mamaye majalisar dokokin tarayya saboda abu 1, bidiyo ya bayyana

NLCHeadquarters
'Yan NLC sun aikawa Bola Tinubu takardar bukatu Hoto: @NLCHeadquarters, @officialABAT
Asali: Twitter

Jerin bukatun kungiyar NLC

1. Daukar matakai domin rage radadin wahala kuma a bude hanyar samun abinci a gida.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Bude iyakoki domin shigo da abinci, siminti da sauran muhimman kayayyakin amfani.

3. Matakan gaggawa da za su tabbatar da samun abinci, a tsare gonaki domin a iya yin noma.

4. Shawarar cire duk wani nau’in haraji da ake karba daga hannun ‘yan kasuwa a kananan hukumomi da jihohi.

5. Gaggawar fara aiwatar da yarjejeniyar da aka cin ma a ranar 2 ga watan Oktoba 2023 da gwamnatin nan.

6. Gaggawar sayo motoci masu amfani da gas da masu amfani da wutar lantarki a duka jihohin Najeriya.

7. A yi gagawar samar da kayan aikin sauya motoci daga shan fetur zuwa gas domin a komawa CNG.

8. Kafa wani kwamitin masu tuwa da tsaki da zai rika sa ido a kan duka tsare-tsaren tallafin gwamnati.

Kara karanta wannan

Kungiyar kwadago ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan tsadar rayuwa

9. A kai wannan yarjejeniya a duka matakai domin tabbatar da tallafin da ake kawowa sun kai ga talaka.

10. A janye kuma a dakatar da karin duk wani kudin makaranta da aka yi a fadin kasar nan.

11. Rage kudin shigo da muhimman magunguna da sauran kayan asibiti domin marasa lafiya.

12. A umarci gwamnatocin jihohi su biya duk wani bashin albashi, alawus, giratuti, fansho da kyau.

13. A fara biyan kudin da aka yi alkawari ga marasa galihu da ake da sunayensu a rajista.

14. Yafe haraji ga duka ma’aikatan gwamnati da ke karbar abin da bai wuce N100, 000 ba.

15. A rage harajin PAYE ga masu karbar albashin da bai wuce N500, 000 a kowane wata ba.

16. Cire harajin VAT a kan kayan masarufi.

17. Bada umarnin amfani da kaya da ayyukan gida domin a kirkiro ayyukan yi.

18. Bada umarnin rage kudin da ake kashewa wajen tafiyar da gwamati.

19. Dakatar da aiwatar da manfufofin hukumar IMF da bankin duniya a Najeriya.

Kara karanta wannan

Sabuwar dokar CBN ta jawo surutu a yunkurin maido darajar Naira a kan Dala

20. A yi saurin kammala tattaunawa a kan maganar karin albashin ma’aikata.

Gwamnati ta karyata zancen juyin mulki

Ana ta yawo da labarai cewa an ankarar da sojoji game da shirin kifar da gwamnatin tarayya, Ministan labarai na kasa ya karyata zancen.

Mohammed Idris ya ja kunnen mutanen da ke kawo maganar kawo karshen mulkin farar hula, ya kuma nuna za a dauki mataki a kansu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng