"Ba Maganar Albashi Bane" Ƴan Ƙwadago Sun Bayyana Abu 1 da Ya Sa Suka Fito Zanga-Zanga a Najeriya

"Ba Maganar Albashi Bane" Ƴan Ƙwadago Sun Bayyana Abu 1 da Ya Sa Suka Fito Zanga-Zanga a Najeriya

  • Ƴan kwadago sun bayyana cewa babban dalilin wannan zanga-zanga da mambobi suka fito shi ne yunwar da ƴan kasa ke ciki
  • Joe Ajaero ya ce batun mafi ƙarancin albashi abin dubawa ne amma ba shi ne asalin abinda ya haddasa NLC fara zanga-zangar kwana biyu ba
  • Shugaban NLC na ƙasa ya ce majalisar dinkin duniya ta ce akalla dala biyu zata ciyar da mutum ɗaya a kowace rana a yanzu

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Ƙungiyar kwadago ta ƙasa (NLC) ta bayyana cewa mambobinta sun fara zanga-zangar kwanaki biyu ne sabida halin yunwar da ƴan Najeriya suka shiga.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, NLC ta ce wannan zanga-zangar da suka fara ba ta da alaƙa da batun sake duba mafi ƙarancin albashin ma'aikata.

Kara karanta wannan

Sabon gwamnan CBN da tawagarsa ne suka jefa ƴan Najeriya cikin tsadar rayuwa? Gaskiya ta fito

Shugaban NLC, Joe Ajaero.
"Muna zanga-zanga ne saboda yunwa, ba wai ƙarancin albashi ba" Shugaban NLC Hoto: Nigerian Labour Congress
Asali: Twitter

Duk da gwamnatin tarayya ta zauna da ƙungiyar kwadago NLC domin daƙile wannan zanga-zanga, taron na su ya karkare ba tare da samun matsaya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Menene maƙasudin zanga-zangar NLC?

Da yake jawabi ranar Talata, shugaban NLC, Joe Ajaero, ya ce sabanin yadda wasu ke ikirari, kungiyar ba ta tsiri wannan zanga-zangar kawai kan a ƙara mafi karancin albashi na N30,000.

Yayin da yake hira da manema labarai a Abuja, Ajaero ya ce:

"Ya kamata ku fahimci cewa muna wannan zanga-zanga ne saboda yunwar da ake fama da ita, wane hali waɗanda ba su samu aiki ba suke ciki? Yaushe za a ƙarƙare batun mafi ƙarancin albashi?"
"Wane sabon mafi karancin albashi za a kawo wanda zai magance yunwa? Majalisar ɗinkin duniya ta ce kowane mutum mafi talauci ya kamata a ciyar da shi akan dala 2 a kowace rana.

Kara karanta wannan

Dandutse: Ƴan bindiga sun kashe babban soja da wasu jami'ai biyu, sun tafka ɓarna kan bayin Allah

"Wannan shine mafi talauci. Kuma idan kana da iyali mai mutum shida, $2 a kowace rana sau shida, ya kama dala 12 kenan. A wata ɗaya ya kama $360, ma'ana N700,000 a kuɗin Najeriya."

Shugagan NLC ya kara da cewa wannan adadin kuɗin ne zasu rike mutum mai iyalai 6 a wata ɗaya wanda a yanzu mafi ƙarancin albashi shi ne N30 000.

A rahoton The Nation, Ajaero ya ci gaba da cewa:

"Kamar yadda kuka sani bamu zamu faɗa musu yadda zasu yi ba, iya ka dai mu gaya musu yadda muke ji ana fama da yunwa a ƙasar nan."

Ƴan kwadago sun kutsa NASS

A wani rahoton Masu zanga-zanga sun yi tururuwa a majalisar dokokin tarayya domin nuna bacin ransu kan halin da ake ciki na tsadar rayuwa a Najeriya.

Shugaban 'yan kwadago ta kasa, Joe Ajaero ne ya yi wa mambobin kungiyarsa jagoranci inda suke kokarin isar da kokensu ga shugabannin majalisar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel