Abubuwa 15 Da Aka Amince Da Su Kafin NLC Da TUC Su Dakatar Da Yajin-Aiki a Jiya

Abubuwa 15 Da Aka Amince Da Su Kafin NLC Da TUC Su Dakatar Da Yajin-Aiki a Jiya

  • Shugabannin kungiyoyin NLC da TUC sun hakura da zuwa yajin-aiki har zuwa nan da wata daya
  • Kafin ‘yan kwadago su lashe amansu, sai da aka cin ma wasu yarjejeniya da gwamnatin Najeriya
  • Bangarorin biyu sun yarda da karin kudi a albashin ma’aikata, kuma za a samar da motocin CNG

Abuja - Kungiyoyin kwadago sun amince su dakatar da shiga yajin-aiki sai nan da wata guda, a sakamakon zama da aka yi da gwamnati.

A karshen tattaunawar da wakilan gwamnatin tarayya su ka yi da kungiyoyin ma’aikata, an hakura da shiga yajin-aiki a kan tsadar fetur.

Olusegun Dada wanda ya na cikin hadiman Mai girma Bola Tinubu, ya jero duka abubuwan da aka cin ma kafin a kai ga cin ma matsaya.

'Yan NLC
'Yan NLC sun fasa yajin-aiki Hoto: Getty Images
Asali: Getty Images

Yarjejeniyar gwamnati da 'yan kwadago

1. Karin N35, 000 a albashin duka ma’aikatan gwamnatin tarayya daga watan Satumba.

Kara karanta wannan

NLC da TUC Sun Fasa Yajin-Aiki, Kungiya Ta Umarci Ma’aikatanta Su Tafi Ofis a Yau

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

2. Dakatar da harajin VAT a kan dizil na tsawon watanni shida.

3. Kafa kwamitin karin albashi nan da kwanaki 30.

4. Ware Naira biliyan 100 domin motoci masu amfani da gas (CNG)

5. Aiwatar da dabarun rage haraji ga ma’aikatan gwamnati da ‘yan kasuwa.

6. Shawo karshen rikicin shugabancin kungiyoyin NURTWA da RTEAN.

7. Kai maganar bashin albashin ma’aikatan manyan makarantu zuwa ga ma’aikatar kwadago.

8. Biyan N25, 000 ga gidaje miliyan 15 na tsawon watanni uku.

9. Kara fitowa da tsare-tsaren bada tallafin taki ga manoma.

10. Karfafawa gwamnatocin jihohi gwiwa wajen kara kudi a albashi.

11. Samar da kudi domin kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa.

12. Ziyarar hadaka domin duba aikin gyaran matatun man Najeriya.

13. Amincewa da yin zama domin tattaunawa nan gaba.

14. Amfani da takardar yarjejeniyar a matsayin hujja a kotu.

15. Dakatar da shirin shiga yajin-aiki na tsawon kwanaki 30.

Wadanda aka yi zaman NLC/TUC da su

Kara karanta wannan

NLC Da TUC Sun Janye Tafiya Yajin Aikin Gama Gari Na Tsawon Kwanaki 30 Bayan Ganawa Da FG

Kwamred Joe Ajaero, Kwamred Emmanuel Ugboaja, mni, Injiniya Festus Osifo da Kwamred Nuhu A. Toro su ka wakilci ‘yan kwadago.

Daga bangaren gwamnati akwai ministocin tarayya; Simon Bako Lalong, Hon. Dr Nkeiruka Onyejeocha da Mallam Mohammed Idris.

Asirin gwamnatin tarayya ya tonu

Gwamnoni sun gano yadda aka rika cire kudi daga asusun ECA, kusan N4tr gwamnatin tarayya ta dauka ba tare da saninsu a Najeriya ba.

A sakamakon haka, za a aikawa duka Gwamnonin Jihohi Naira Tiriliyan 1 na kudin rarar danyen mai, za a rika biyan kudin nan ne sannu a hankali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel