Kungiyar Kwadago Ta Fara Gudanar da Zanga-Zangar Gama Gari Kan Tsadar Rayuwa

Kungiyar Kwadago Ta Fara Gudanar da Zanga-Zangar Gama Gari Kan Tsadar Rayuwa

  • Kungiyar kwadago ta fara zanga-zangar gama gari saboda tsadar rayuwa da ake fama da shi a Najeriya
  • Mambobin kungiyar sun mamaye unguwanni a jihar Legas, a yau Talata, 27 ga watan Fabrairu, domin nuna bacin ransu kan halin da ake ciki na matsin tattalin arziki
  • An dai yi zama tsakanin kungiyar da gwamnatin tarayya a ranar Litinin, amma aka tashi baran-baran ba tare da an cimma matsala daya ba

Aisha Musa ta shafe tsawon shekaru tana kawo labaran Hausa a bangaren siyasa, tsegumi da al’amura

Jihar Lagos - Kungiyar kwadago ta kasa ta fara gudanar da zanga-zangar gama gari kan mawuyacin halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kungiyar TUC ta ce ba za ta shiga wannan zanga-zangar ta 'yan kwadago ba.

Kara karanta wannan

NLC ta yi bazaranar ɗaukar mataki 1 idan aka farmaki masu zanga-zangar lumana a ƙasar

'Yan kwadago sun fara yajin aiki
Kungiyar Kwadago Ta Fara Gudanar da Zanga-Zangar Gama Gari Kan Tsadar Rayuwa
Asali: Twitter

Mambobin kungiyar NLC sun mamaye unguwanni a jihar Legas domin nuna bacin ransu kan tsadar rayuwar da ake fama da shi a kasar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

'Yan kwadagon na kuma zanga-zanga akan gazawar gwamnati, wajen aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a ranar 2, ga watan Oktoban 2023, bayan cire tallafin man fetur.

Me yasa kungiyar kwadago ke zanga-zanga a Najeriya?

Wannan mataki ya biyo bayan cikar wa'adin kwanaki 14 da suka bai wa gwamnatin tarayya domin ta dauki matakai kan mawuyacin halin da al'ummar kasar ke ciki.

An tashi baran-baran a taron da aka yi tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago a daren jiya Litinin, inda kungiyar ta sha alwashin fara zanga-zangar da ta yi niya.

Mambobin kungiyar ta NLC da yawansu sun mamaye karkashin gadar Ikeja, inda aka gano su suna wake-wake da raye-raye yayin da suke kira ga gwamnati da ta saurari bukatunsu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kafa kwamiti mai bangarori uku na ba shi shawara kan tattalin arziki

Ana sanya ran zanga-zangar za ta ci gaba a gobe Laraba, 28 ga watan Fabrairu, jaridar Punch ta ruwaito.

NLC ta mika bukatarta wajen gwamnati

A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnatin tarayya ba ta iya shawo kan kungiyar ‘yan kwadago ta kasa watau NLC ta fasa shirya zanga-zangarta ba.

Duk da an zauna da manyan jami’an gwamnati, The Cable ta ce shugabannin ma’aikatan sun cije sai sun cigaba da zanga-zanga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel