‘Dan APC Ya Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin da Talaka Yake Ciki, Ya Nemi a Dauki Mataki

‘Dan APC Ya Fadawa Tinubu Gaskiyar Halin da Talaka Yake Ciki, Ya Nemi a Dauki Mataki

  • Hon. Olatunbosun Oyintiloye yana cikin ‘ya ‘yan jam’iyyar APC, amma ya fito ya koka a kan tsadar rayuwa
  • ‘Dan siyasar ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu ya dauki mataki kan yadda farashin magunguna su ke tashi
  • Magungunan da marasa lafiya su ka saba saye, ya fi karfin talaka a yau saboda tsadan kaya a kasuwa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Osun - Olatunbosun Oyintiloye wanda za a iya kiransa jigo a jam’iyyar APC ta reshen jihar Osun, ya yi kira ga Bola Ahmed Tinubu.

Vanguard ta rahoto cewa Olatunbosun Oyintiloye ya kai kuka wajen Mai girma Bola Ahmed Tinubu a game da tsadar magunguna.

Bola Tinubu
An fadawa Bola Tinubu magunguna sun tashi Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu/istockphoto
Asali: Facebook

Tinubu ya sa baki a kan tsadar magani

Kara karanta wannan

Jigon APC ya bayyana abu 1 tak da zai jawo wa Tinubu faduwa a 2027, ya ba da shawara

‘Dan siyasar ya ce a halin yanzu magunguna sun yi tsada sosai, saboda haka ya kamata shugaban kasa ya sa baki domin a samu sauki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mai ba tsohon gwamnan jihar Osun Gboyega Oyetola shawara ya yi wannan kira ne lokacin da ya zanta da manema labarai a ranar Lahadi.

Yayin da yake jawabi a garin Osogbo a karshen makon jiyan, ‘dan siyasan ya ce mutane da-dama ba su iya sayen muhimman magunguna.

Menene ya jawo farashin kaya su ka tashi?

Oyintiloye yana ganin cewa farashin sun tashi ne saboda wasu dalilai, daga ciki shi ne kamfanoni irinsu GSK za su daina yin aiki a Najeriya.

Baya ga tserewar da wasu kamfanoni su ke yi, ana fama da masifar tsadar kaya tun da aka karya farashin Naira da aka kafa sabuwar gwamnati.

The Guardian ta rahoto ‘dan siyasar yana cewa NBS ta tabbatar da farashin magungunan da aka shigo da su ya karu da 68% a yanzu.

Kara karanta wannan

‘Yan Shi’a sun taso sojoji, sun nemi hukunta sojojin da suka kashe 'Yan Maulidi

Yadda marasa lafiya su ke shan wahala

Magunguna irinsu amlodipine, augmentin, paracetamol, exforge da Coartem da aka saba saye, suna nema su karfin marasa lafiya a yau.

Tsohon ‘dan majalisar ya nuna baya ga tsadar magunguna, dama talakawa na fama da wahalar tashin kudin kasar waje da farashin mai.

Masu hawan jini, ciwon sukari, tarin tibi suna cikin wadanda su ka fi shan wahala.

Meya jawo tsadar magunguna?

Mun tuntubi Pharm. Ahmad Abubakar a garin Bauchi domin ya yi mana bayanin abin da ya jawo tashin farashi, ya ce har da tsadar mai.

Masanin harkar magungunan ya shaidawa Legit akwai tasirin tashin fetur da dizil wajen jigilar kaya da kuma ficewar wasu kamfanoni.

Ahmad Abubakar ya ce kamfanin GSK da ya dade a Najeriya ya bar kasar saboda haka ne magunguna irinsu augmentin su ka kara kudi.

Magungunan N5000 zuwa N7000 sun koma kusan N20000 a yau yayin da farashin Seritide Inhaler ya nunku kusan hudu zuwa N50, 000.

Kara karanta wannan

Wike v Fubara: Asalin dalilin ‘Yan majalisan Ribas na dawowa APC Inji Jagororin Jam’iyya

Haka kuma kamfanin Sanofi sun bar aiki a Najeriya, dole magungunansu su kara kudi.

Kungiya za ta goyi bayan Tinubu

Ahmad Sani Yariman Bakura da wasu ‘yan adawar Bola Tinubu sun hakura za su bi bayan shi a APC kamar yadda rahoto ya zo a dazu.

Domin ganin APC ta cigaba da mulki bayan 2027, za a kafa kungiyar da za ta taimaki Shugaban kasa saboda an gamsu da manufofinsa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel