Kotu Ta Daure Tsohon Manajan Banki Shekaru 121 a Gidan Kaso, Ta Fadi Dalilai

Kotu Ta Daure Tsohon Manajan Banki Shekaru 121 a Gidan Kaso, Ta Fadi Dalilai

  • Wani tsohon manajan bankin FCMB ya shiga matsala bayan kotu ta yanke masa hukuncin shekaru 121 a gidan yari
  • Kotun ta yanke hukuncin ne bayan zargin Nwachukwu Placidus da badakalar N112m na wani kwastoma a bankin Idemili Microfinance
  • Nwachukwu ya musanta zargin bayan karanto masa dukkan tuhume-tuhumen da ake yi masa yayin da yake jagorancin bankin

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Anambra - Babbar kotu a jihar Anambra ta daure tsohon manajan bankin FCMB a Onitsha shekaru 121 a gidan kaso.

Kotun ta dauki matakin ne kan Nwachukwu Placidus bayan zarginsa da sace kudin kwastoma har N112m a bankin.

Kotu ta yanke hukuncin daurin shekaru 121 kan tsohon manajan banki
Kotu a jihar Anambra ta daure tsohon manajan banki shekaru 121 a gidan kaso. Hoto: Africom.
Asali: Facebook

EFCC ta gurfanar da wanda ake zargi

Kara karanta wannan

Badakalar N2.1trn: Jerin tsofaffin gwamnoni 54 da EFCC ke tuhuma kan zargin almundahana

Hukumar EFCC reshen jihar Enugu ne ta gurfanar da Nwachukwu tun a watan Maris din 2018 kan tuhume-tuhume guda 16.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Alkalin kotun, S. N. Odili shi ya yanke wannan hukunci bayan karanto lafuffukan da ake zargin Nwachukwu.

Hukumar EFCC ita ta bayyana haka a shafinta na Facebook a yau Asabar 4 ga watan Mayu.

Bayan kammala karanto tuhume-tuhumen, Nwachukwu ya musanta aikata laifuffukan da ake zarginsa.

Lauyan hukumar EFCC, Mainforce Ekwu ya gabatar da shaidu guda hudu da takardu da ke tabbatar da laifuffukan da Nwachukwu ya aikata.

Daga bisani alkalin kotun ya ce shaidun da aka gabatar sun tabbatar da dukkan zargin da ake yi wa Nwachukwu.

Wane hukunci kotun ta yankewa Nwachukwu?

Daga nan ne sai Mai Shari'a, S. Odili ya yanke masa hukuncin shekaru 121 kan dukkan korafe-korafen da ake yi kansa.

Kara karanta wannan

"Buhari ya daura shugaban APC duk da zargin cin N15bn", Tsohon Minista ya tona asiri

Har ila yau, kotun ta umarci wanda ake zargin ya tabbatar da mayar da dukkan kudin da ya ci ga bankin Idemili Microfinance.

Kotu ta umarci kama tsohon soja

A wani labarin, mun baku labarin cewa Babbar Kotun Tarayya ta umarci kama tsohon hafsan sojojin ruwa a Najeriya, Usman Jibrin kan badakalar makudan kuɗi.

An zargin Jibrin da wasu mutane biyu da karkatar da makudan kudi har N1.5bn lokacin da suke gidan soja.

Kotun ta ba da umarnin bayan hukumar yaki da cin hanci ta ICPC ta gurfanar da wadanda ake zargin a gabanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel