An Dakatar da Fitaccen Basarake Kan Zargin Cin Zarafin Darajar Naira, Ya Yi Magana Kan Matakin

An Dakatar da Fitaccen Basarake Kan Zargin Cin Zarafin Darajar Naira, Ya Yi Magana Kan Matakin

  • Kwamitin sarakunan gargajiya na Egba da ke jihar Ogun ya dakatar da wani basarake kan cin zarafin naira
  • An dakatar da Olu na Owode, Oba Kolawole Sowemimo kan zargin zubar da mutuncin naira yayin da ake taro
  • Oba Kolawole ya tabbatar da hakan ne a yau Asabar 17 ga watan Faburairu inda ya ce an dakatar da shi har watanni biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Ogun - Olu na Owode, Oba Kolawole Sowemimo ya tabbatar da samun hukuncin dakatar da shi daga kujerarsa.

Oba Kolawole ya tabbatar da hakan ne a yau Asabar 17 ga watan Faburairu inda ya ce an dakatar da shi na tsawon watanni biyu a jihar Ogun.

Kara karanta wannan

A karshe, Tinubu ya janye tuhumar da ake kan dan takarar shugaban kasa da Buhari ya gurfanar

An dakatar da babban basarake kan wani dalili
An Dakatar da Basarake a Jihar Ogun Kan Cin Zarafin Kudin Naira. Hoto: Oba Kolawole Sowemimo.
Asali: Facebook

Mene dalilin dakatar da basaraken a Ogun?

Kwamitin sarakunan gargajiya na Egba shi ya dauki matakin bayan zargin cin zarafin naira, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Basaraken ya yayinyayi zantawa da wakilin Punch, ya ce an sanar da dakatar da shi daga kujerarsa ne a jiya Juma'a 16 ga watan Faburairu.

A cewarsa:

"Sun tabbatar da cewa an dakatar da ni ne saboda yadda na watsa kudade kan wani mawaki.
"Lokacin da suka tambaye ni ko ina da abin cewa, na tashi na nemi afuwarsu kan abin da na aikata.
"Dalilin haka dakatarwar da aka sanar tun farko na watanni uku babu albashi, an rage zuwa watanni biyu."

Martanin basaraken kan matakin

Ya kara da cewa:

"Na amince kuma na karbi wannan hukunci da aka yanke saboda wanda muke so ne muke masa hukunci, na gamsu da matakin."

Kara karanta wannan

Murna yayin da gwamnan APC ya fara raba kayan tallafi na biliyan 5 ga mabukata

Idan ba a manta ba a farkon watan Janairu ne aka gano basaraken ya na watsa kudade kan mawaki, Wasiu Ayinde da takardun dubu-dubu.

Kwamitin sarakunan sun yi Allah wadai da abin da basaraken ya aikata wurin zubar da darajar naira.

Sun tabbatar da cewa aikata hakan ya sabawa dokokin Babban Bankin Najeriya, CBN, cewar Trust Radio.

'Yan bindiga sun hallaka sarakuna 2

Kun ji cewa wasu 'yan bindiga sun yi ajalin wasu sarakunan gargajiya biyu a jihar Ekiti yayin wani hari.

Maharan sun farmaki sarakunan gargajiya uku yayin da suke dawowa daga taron samar da tsaro a yankin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel