Gwamnan Najeriya Ya Dakatar da Basarake Bisa Nada Sanata Sarauta

Gwamnan Najeriya Ya Dakatar da Basarake Bisa Nada Sanata Sarauta

  • An shiga wani yanayi a yayin da Gwamnan jihar Anambra, Soludo ya dakatar da sarkin masarautar Neni
  • Rahotanni sun bayyana cewa an dakatar da basaraken ne awanni bayan na da Sanata Ubah sarautar 'Odenjinji Neni'
  • Gwamnan ya ce basaraken ya karya dokar masarautun jihar da ta haramta irin wannan nadin sarauta da ya yi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Anambra - Gwamnan jihar Anambra ya dakatar da sarkin Neni, Damian Ezeani saboda ya yi wa Ifeanyi Ubah, sanata mai wakiltar Anambra ta Kudu nadin sarautar gargajiya.

Neni wani gari ne da ke a karkashin karamar hukumar Anaocha da ke jihar Anambra, a Arewa maso Gabashin Najeriya.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Tsohon Atoni-janar a jihar Arewa ya riga mu gidan gaskiya da shekaru 81

Gwamna ya dakatar da basarake a Anambra
Gwamnan Anambra ya tube rawanin sarkin Neni, Damian Ezeani saboda ya nada sanata sarauta. Hoto: The TC Chairman, Anaocha
Asali: Facebook

An fitar da sanarwar dakatar da Sarkin Neni

Kwamishinan kananan hukumomi masarautu na jihar, Tony-Collins Nwabunwanne, ya bayyana hakan a wata wasika da aka aika wa basaraken.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An kuma rarraba wasikar zuwa ga kwamishinan 'yan sanda na jihar da hukumar tsaro ta farin kaya DSS a ranar 8 ga watan Janairu.

Premium Times ta ruwaito cewa basaraken ya nada Sanata Ubah sarautar 'Odenjinji Neni' a ranar Litinin, awanni kadan kafin dakatar da shi.

Me ya yi zafi har aka dakatar da basaraken?

Mr Nwabunwanne a cikin wasikar ya ce basaraken ya karya dokar masarautun jihar Anambra da ta haramta nada mukamin sarauta ga wanda ba dan yankin masarauta ba.

Dokar masarautar ta ce duk wani basarake da ke son ba da mukamin sarauta ga wanda ba dan yankinsa ba, sai ya nemi izini daga basaraken waccan yankin don gudun husuma.

Kara karanta wannan

"Ba zama": Gwamnan jihar Arewa ya yi ganawar sirri da Shugaba Tinubu a Abuja, an gano dalili

Haka zalika dokar za ta taimaka wajen dakile ba da mukamin sarauta don neman kudi, da kuma nadin sarauta barkatai ga wadanda ba su dace ba.

Sakon gwamna ga Sarkin Neni da aka dakatar

Gwamnan jihar ya gargadi Damian Ezeani da ka da ya kuskura ya kara bayyana kansa matsayin sarkin Neni har zuwa lokacin da aka janye dakatarwar.

Ya nemi basaraken ya tuba daga laifin da ya aikata, ya kuma rubuta wa gwamnan dalilin da zai hana a tumbuke rawaninsa na sarki, rahoton Politics Nigeria.

An warware rawanin sarkin Hausawa, Haruna Maiyasin

A wani labarin makamancin wannan, kun ji cewa an dakatar da Sarkin Sasa, Haruna Maiyasin saboda kamashi da laifin rashin ladabi ga Sarki Olubadan.

Haruna Maiyasin shi ne sarkin Hausawan kasar Ibadan, kuma an zarge shi da yin nade-naden sarauta ba tare da neman izinin babban sarki ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel