Hanyoyi guda 10 na yadda ake amfani da ganyen mangwaro wajen magani

Hanyoyi guda 10 na yadda ake amfani da ganyen mangwaro wajen magani

- Mangwaro na daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake ci wanda ke dauke da sinadarai masu matukar amfani

- Bayan maganin yunwa da magwaro ke yi, tana dauke da sinadaren Potassium, Copper, Magnesium

- Nahiyar Asia sun fi amfani da ganyen mangwaro wajen maganin miyagun cutukan da kan addabi dan Adam

Mangwaro na daga cikin ‘ya’yan itatuwan da ake ci wanda ke dauke da sinadaren inganta kiwon lafiyar mutum.

A cikin mangwaro, akwai sinadarin Vitamin C wanda ke warkar da mura, rauni da sauransu. Sannan akwai sinadarin Copper wanda ke kare mutum daga kamuwa da cututtuka. Potassium wanda ke inganta motsa jiki da Magnesium wanda ke kaifafa kwakwalwa.

Bayanai sun nuna cewa nahiyar Asia sun fi amfani da ganyen mangwaro wajen warkar da cututtuka saboda ingancin da yake da shi.

KU KARANTA: Ango yace allan fur ya fasa auren amaryarshi bayan ya gano sun kai shi wajen bokaye da 'yan bori ita da mahaifiyarta

Ga kadan daga cikin amfanin ganyen magwaro:

1. Ganyen mangwaro na kawar da cutar siga wato ‘Dibetes’

Ganyan mangwaro na warkar da cutar siga ne idan aka shanya shi ya bushe sannan aka jika garin a ruwa sai a rika sha.

2. Yana kawar da hawan jini.

Ana yin amfani da garin busashen ganyen mangwaro, sai a rika diba ana dafa shi ana sha kamar shayi. Haka zai taimaka wajen kawar da hawan jini.

3. Yana warkar da cutar koda

Shan ruwan ganyen magwaro da aka jika na warkar da cutar Koda.

4. Yana warkar da matsalolin da ke han numfashi.

Idan aka hada ruwan ganyen mangwaro da zuma, ana samun lafiya ga mura da cutar Asma.

5. Yana kawar da atini.

Shima idan aka sha ruwan zai taimaka wajen dakatar da Atini.

6. Yana dakatar da shakuwa.

Mai fama da shakuwa zai warke idan ya shaki hayakin ganyen mangwaro.

7. Mai fama da rashin natsuwa wato ‘Anxiety’ zai samu sauki idan yana shan ruwan ganyan mangwaro.

8. Mai fama da ciwon ciki zai sami sauki idan yana shan ruwan dafaffen ganyen kullum safe kafin a ci abinci.

9. Yana warkar da ciwon kunne.

Ruwan dake cikin ganyen mangoro na dauke da sinadarin warkar da ciwon kunne wanda idan aka diga a kunnen dake ciwo zai warke.

10. Ganyen mangwaro na warkar da kuna

Ana amfani da tokan ganyen mangwaro a shafa a kan rauni don a warke.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel