Titin Abuja-Kaduna da Buhari Ya Bada a Kan N165bn Ya Koma N1.35tr – Ministan Tinubu

Titin Abuja-Kaduna da Buhari Ya Bada a Kan N165bn Ya Koma N1.35tr – Ministan Tinubu

  • David Umahi ya yi zama da darektocin ma’aikatar ayyuka na tarayya, an tattauna game da titin Abuja- Kano
  • Ministan ayyukan kasar ya ce akwai sashen da ba a karasa a kan hanyar ba daga birnin Abuja zuwa jihar Kaduna
  • Sanata Umahi ya ce kamfanin Julius Berger da aka ba aikin sun dawo suna neman N1.35tr domin su karasa titin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abuja - Ministan ayyuka, David Umahi, ya ce kamfanin Julius Berger suna bukatar karin kudi domin kammala aikin titin Abuja-Kaduna.

Labari ya zo a Daily Trust cewa Sanata David Umahi ya ce Julius Berger na ikirarin sashen aikin na hanyar Abuja-Kano zai ci masu N1.35tr.

Titin Abuja
Titin Abuja-Kaduna-Kano Hoto: @FMWNIG
Asali: Twitter

Ministan ayyuka na tarayyan ya yi bayani da ya zauna da darektocinsa a Abuja a ranar Alhamis, ya ce kwangilar ta tashi daga N165bn.

Kara karanta wannan

NSCDC ta kama fasto da wasu mutane biyu kan damfara a Kogi

Tarihin kwangilar titin Abuja-Kano

Da farko a kan N165bn Babatunde Fashola ya fara bada aikin, daga baya aka mai da shi N645bn a mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yanzu da aikin ya tashi, David Umahi ya ce gwamnati ba ta da kudin biyan kwangilar.

Shekara 7 ba a gama hanyar Abuja-Kaduna ba

A 2017 aka bada kwangilar sake gina hanyar Abuja zuwa Kano, amma ba a iya fara aikin ba sai cikin shekarar 2018 idan ba a manta ba.

An yi niyyar kammala kwangilar a 2021, amma har Muhammadu Buhari ba a gama ba.

Sai dai an yi nasarar karasa bangaren Zariya zuwa Kano da nufin cewa sannu a hankali za a karasa ragowar sashen Abuja zuwa Kaduna.

Yaushe za a gama titin Abuja-Kaduna a 2024?

The Cable ta ce duk da haka gwamnatin Bola Ahmed Tinubu tana sa ran za a gama gaba daya aikin titin a sabuwar shekarar nan ta 2024.

Kara karanta wannan

Attajirin Najeriya Dangote ya sullubo da aka fito da jerin farko na masu kudin 2024

Ministan ya ce a karkashin tsarin shugaban kasa aka yi aikin bayan an gano kudin sata, ya kuma nuna muhimmancin titin ga yankin Arewa.

Wannan yana cikin manyan ayyukan da aka yi a Najeriya a mulkin Muhammadu Buhari.

Binciken gwamnatin tarayya

An ji labari kungiyar NANS ta Benin ta ce akwai dalibai da ke karatu tsakaninsu da Allah a jami’o’in da aka tsaida karbar takardar shaidarsu.

Kungiyar daliban ta roki gwamnatin Najeriya ta guji yin kudin goro, ta hukunta marasa gaskiya kurum a binciken masu digirin bogin waje.

Asali: Legit.ng

Online view pixel