Ba za mu huta ba sai mun kammala titin Abuja-Kaduna-Kano a 2023 – Ministan Buhari

Ba za mu huta ba sai mun kammala titin Abuja-Kaduna-Kano a 2023 – Ministan Buhari

- Ministan ayyuka da gidaje, Aliyu Abubakar ya ce sun dage kan titin Abuja-Kano

- Aliyu Abubakar ya ce gwamnatin Muhammadu Buhari ta na ji da wannan aikin

- Abubakar yake cewa ba za su huta ba sai an kammala gyaran titin a farkon 2023

Karamin ministan ayyuka da gidaje na kasa, Aliyu Abubakar, ya ce gwamnatin tarayya ba za ta huta ba sai an kammala gyaran titin Abuja-Kaduna-Kano.

Jaridar Vanguard ta rahoto Ministan ya na wannan bayani a ranar Alhamis, 11 ga watan Fubrairu, 2021, lokacin da ya kai ziyara ya duba yadda aikin ke tafiya.

Mai girma Ministan ya bayyana cewa ginin titin na Abuja-Kaduna-Kano ya na cikin manyan ayyukan da gwamnatin Muhammadu Buhari ta ke ji da su.

Aliyu Abubakar ya ce mai gidansa, Babatunde Raji-Fashola, ya ziyarci inda ake wannan aiki tare da tawagar gwamnatin tarayya domin su gane wa idanunsu.

KU KARANTA: Yadda rajistar ‘Ya ‘yan APC ya zama abin rigima a Kwara, Osun, da Delta

Abubakar ya ce bayan zuwan Babatunde Fashola, wasu kwararru da kuma tawagar sakataren din-din-din na ma’aikatar tarayyar sun zo sun duba wannan aiki.

“Wannan ya nuna yadda mu ka dage domin ganin an kammala wannan aiki kafin gwamnatin nan ta shude. Za ayi wannan ne domin mun damu da kwangilar.”

“Daga shugaban kasa Buhari, Minista, ni kai na, ma’aikatanmu, kwararru, da ‘yan kwangilar, duk mun dage a kan ganin an karkare wannan aiki.” Inji Abubakar.

“Mun gamu da kalubale, da farko wajen gyaran titin da ake da shi. Amma bayan mun fara aikin, mun ga bukatar a sake gina titin ne gaba daya, a nan mu ke yanzu.”

KU KARANTA: Bayan ya yi wa Buhari ta-tas, Fani-Kayode zai koma APC

Ba za mu huta ba sai mun kammala titin Abuja-Kaduna-Kano a 2023 – Ministan Buhari
Titin Abuja zuwa Kano Hoto: www.julius-berger.com
Source: UGC

“Titin ya dade ba tare da an kula da shi ba, idan ana gyara hanya, ya fi dade wa.” Ministan ya ce ribanya fadin titin ya na nufin za ayi aikin kilomita kusan 800.

Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ce ta amince a gyara wannan muhimmiyar hanya.

Kwanaki kun ji shugaban sashin gini da gyaran manyan tituna na ma'aikatar tarayya ya na cewa za a kammala aikin ginin titin Abuja-Kaduna-Kano a shekarar 2023.

Jami'in ya bayyana haka lokacin da ya ke duba ci gaban aikin a Kano, ya ce an kammala fiye da kilomita dari na aikin duk da cewa ba a jere ake tafiya da titin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

M. Malumfashi ma'aikacin jaridar Legit.ng ne wanda ya shafe kusan shekaru 5 ya na wannan aiki. Ya yi Digirin farko a ilmin komfuta da Digirgir a harkar bayanai (Info Mgt), kuma ya na Digirgir a ilmin aikin jarida.

Malumfashi ya kan buga labarai, ya yi rubuce-rubuce a harkar siyasa, wasanni da addini. Ya yi rubuce-rubuce barkatai a gidajen jaridun Najeriya.

A bibiye shi a Twitter @m_malumfashi

Source: Legit.ng

Online view pixel