NSCDC Ta Kama Fasto da Wasu Mutane Biyu Kan Damfara a Kogi

NSCDC Ta Kama Fasto da Wasu Mutane Biyu Kan Damfara a Kogi

  • Hukumar NSCDC ta samu nasarar cafke wasu mutum uku bisa laifin zamba cikin aminci da damfara
  • Daga cikin wadanda aka kama har da wani fasto wanda ya damfari wani mutum naira miliyan daya
  • Saura mutum biyu an kama su da laifin karbar kudi da buga takardun daukar aiki ba bogi da siyar da motar karya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Jihar Kogi - Hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta cafke mutum uku da suka hada da wani fasto kan laifin sayar da takardun aiki na bogi ga wasu mutane.

Mataimakin babban kwamandan rundunar NSCDC, Ahmad Ahmad Gandi ya bayyana hakan a Lokoja a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun kai hari a wani babban kanti a jihar Nasarawa, sun kashe mutum 4

NSCDC ta kama fasto da mutum 2 a kogi.
Kogi: NSCDC ta cika hannunta da wani fasto da mutum 2 kan laifin damfarar mutane. Hoto: @official_NSCDC
Asali: Twitter

Daily Trust ta ruwaito cewa an cafke Faruk Abdullahi, Fasto Chimezie da Atahiru Abuh bisa laifin damfarar abokan kasuwancin su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Bayani kan laifukan da mutanen uku suka aikata

Da ya ke bayani, Ahmad Gandi ya ce Faruk Abdullahi ne ya sam ar da takardar daukar aikin a hukumar NIMASA ta bogi, inda ya sayar wa Sule Nuruddeen akan naira miliyan biyu.

Shafin Kogi Post ya ruwaito cewa Fasto Chimezie ya karbi naira miliyan daya daga AbdulBanu Ibrahim da ikirarin zai taimaka masa ya fara sana'ar hakar 'coal'.

Shi kuma Atahiru Abuh an kama shi ne bayan karbar naira miliyan daya daga hannun wata Aishat Abuh da ikirarin zai siyar mata da mota.

Hukumar NSCDC ta tsaurara bincike akan mutanen uku

Hukumar NSCDC ta kara da cewa na cafke mutanen uku bayan dogon bincike biyo bayan korafin da aka shigar kan su.

Kara karanta wannan

Mummunan hatsari ya lakume rayukan akalla mutum 6 a babban titin Kaduna zuwa Zariya

Hukumar ta ce bincike ya nuna takardar daukar aiki da Faruk Abdullahi ya sama wa Sule Nuruddeen ta bogi ce.

A cewar Ahmad Gandi, ya ce hukumar ta cafke mai laifin a wata mabuyar sa da ke cikin jihar.

Ki mika kanki tun muna shaidar juna, EFCC ta gargadi Sadiya

A wani labarin kuma, hukumar EFCC ta nemi tsohuwar ministar Buhari, Sadiya Umar Farouk ta mika kanta ba tare da bata lokaci ba.

Ana zargin Umar Farouk da sace akalla baira biliyan 37.1 a lokacin da ta ke ministar jin kai a mulkin tsohon shugaban kasa Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel