Hukumar EFCC Ta Fara Tuhumar Wasu Manyan Ministocin Buhari Kan Badakalar Naira Biliyan 187

Hukumar EFCC Ta Fara Tuhumar Wasu Manyan Ministocin Buhari Kan Badakalar Naira Biliyan 187

  • Da yiwuwar hukumar EFCC ta kama tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk da wasu tsaffin daraktoci, biyo bayan alakanta su da wata badakalar kwangila
  • Binciken hukumar na zuwa ne a yayin da gwamnati ta dage kan magance rashawa da tabbatar da bin kadin kudaden da aka kashe a ma'aikatun gwamnati
  • Badakalar da ta rutsa da ministar jin kai da kawar da fatara ta shafi sama da naira biliyan 37 da ake zargin an yi sama da fadi da ita a gwamnatin Buhari

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

A wani sabon bincike, wani dan kwangila James Okwete ya shiga hannun Hukumar yaki da masu yin ta'annati da tattalin arziki da dukiyar kasa (EFCC).

Kara karanta wannan

“Zan dauki mataki”, Ministar Buhari ta yi wa EFCC martani kan zargin sa hannunta a badakalar N37bn

Hukumar ta kama Okwete ne kan binciken badakalar naira biliyan 37 da ta ke yi da ya shafi ma'aikatar ayyukan jin kai karkashin tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk.

Hukumar EFCC ta tuhumi ministoci 4 kan zambar naira biliyan 187.
Hukumar EFCC ta tuhumi tsohuwar minista Sadiya Umar-Farouk da wasu ministoci 3 kan zambar naira biliyan 187. Hoto: @officialEFCC, @Sadiya_farouq
Asali: Twitter

Wani babban jami'in EFCC ne ya sanar wa jaridar The Punch hakan a ranar Lahadi, 24 ga watan Disamba 2023.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar majiyar, dan kwangilar ya bayar da wasu muhimman bayanai game da Umar-Farouk da wasu tsaffin daraktoci a ma'aikatar.

Badakalar naira biliyan 187: An tsoma ministoci 4 na mulkin Buhari

Idan ba a manta ba, an ruwaito yadda EFCC ta gano badakalar naira biliyan 37 da aka yi a ma'aikatar jin kai lokacin mulkin Muhammadu Buhari.

Bincike ya nuna cewa an cire kudin daga asusun gwamnatin tarayya, an tura wa bankuna 38 da su ke da alaka da dan kwangilar James Okwete.

Kara karanta wannan

Kirsimeti: Sanatar Arewa ta raba wa 'yan mazabarta tirelar shinkafa 6 da sauran kaya, ta yi gargadi

Ana tuhumar Okwete da yin hada-hadar kudi ba bisa ka'ida ba, da suka hada da tura naira biliyan 6.7 zuwa ga wasu 'yan canji da kuma cire tsabar kudi har naira miliyan 540 daga banki, da sauran su.

Wannan na zuwa yayin da hukumar ke binciken wasu ministoci uku, wadanda suka yi aiki karkashin tsohon shugaban kasa Buhari da ake zargin sun wawure naira biliyan 150.

Yadda bankuna suka cire naira biliyan 150 daga asusun jama'a

A wani labarin, bankuna da sauran cibiyoyin hada-hadar kudade a Najeriya sun saka naira biliyan 156.94 matsayin kudin harajin VAT a asusun gwamnatin tarayya.

Wannan adadin kudin ya karu da kaso 13.63% idan aka kwatanta shi da naira biliyan 78.77 da bankunan suka tura wa gwamnati a shekarar 2022.

Asali: Legit.ng

Online view pixel