Naira Ta Sake Sunkuyawa, Darajar Dala Ta Cigaba da Tashi Zuwa N1030 a Kasuwar Canji

Naira Ta Sake Sunkuyawa, Darajar Dala Ta Cigaba da Tashi Zuwa N1030 a Kasuwar Canji

  • Ana tunanin Dala za ta sauka a karshen shekara, amma har yanzu alamu sun nuna darajar kudin ya na ta karuwa ne
  • Wasu ‘yan kasuwar canji sun saida kowace Dalar Amurka a kan N1, 030, Naira ta kara rasa kima daga Laraba zuwa jiya
  • Wadanda su ka saye Dala kwanakin baya domin su ci riba, sun samu makudan kudi da su ka saida ta a makonnin nan

Abuja - A ranar Alhamis, Naira ba ta ji da dadi ba a kasuwar canji domin kudin Najeriyan ya na cigaba da kara rasa daraja da kima.

Vanguard ta fitar da rahoto da ya nuna cewa sai da ‘yan kasuwar canji su ka saida duk $1 a kan N1,030, an samu karin kusan N20.

Kafin nan, ‘yan BDC da ke harkar canjin kudi sun saida Dala a N1, 010 a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Shinkafa Da Jerin Duka Kaya 43 Da CBN Ya Halatta Karbar Dala a Shigo Da Su

Dalar Amurka
Gwamnan CBN Mr. Yemi Cardoso a lokacin ya na Citibank Hoto: @GreaterLagosNG
Asali: Twitter

$1 a karkashin sabon Gwamnan CBN

A maimakon Naira ta mike kamar yadda gwamnan bankin CBN ya ke sa rai, kudin Najeriyan ya cigaba da rasa daraja kan Dalar Amurka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin farin cikin shi ne Naira ta tashi a kafar I & E da bankin CBN ya kirkiro domin saida kudin kasashen waje ga ‘yan kasuwa a kasar.

Dalar Amurka ta sauka a kafar I & E

Da aka tashi a kasuwa jiya, rahoton da aka fitar ya ce an yi cinikin Dala ne a kan N759.2.

Bayan da aka samu daga FMDQ ya nuna Dalar ta karye da akalla N17.16 tun da farashin ta ya sauka daga N776.8 zuwa N759.2 a jiya.

Daidaita farashin Dala zai yiwu?

Yayin da ake farin ciki da saukin da aka samu a I & E, tazarar da ke tsakanin farashin kasuwa da na banki ya karu a karshen makon nan.

Kara karanta wannan

CBN Ya Bayyana Abu 1 Tak Da Ya Yi Na Dawo da Darajar Naira a Kasar, Ya Fadi Adadin Kudin da Ya Zuba

Daga ratar N233.2 da ke tsakanin farashin biyu, yanzu abin ya koma N270.8. Wannnan ya nuna har yanzu akwai aiki a gaban CBN.

Legit ta na da labari an saida dala a kasuwa a kan sama da N1, 000 a jihar Kaduna.

Hakan ya na zuwa ne a lokacin da aka ji wasu ‘yan kasuwar canji da ke garin Abuja sun yi taro, sun karya farashin Dalar zuwa N900.

Bankin CBN ya cire takunkumi

A halin yanzu ana fama da tashin farashin kaya a kasuwa da kuma tsadar dala a kasar nan, sai aka ji labari CBN ta dauki mataki.

Yanzu bankin CBN zai iya ba ‘dan kasuwa kudin kasashen waje domin ya shigo da kayan da aka haramta lokacin Muhammadu Buhari.

Asali: Legit.ng

Online view pixel