Sojoji Sun Saki Bam Sun Kashe Mutane a Wajen Maulidin Annabi SAW a Kaduna

Sojoji Sun Saki Bam Sun Kashe Mutane a Wajen Maulidin Annabi SAW a Kaduna

  • Ana tsoron bam ya hallaka mutane sama da 30 a tashi guda a wani kauye da yake jihar Kaduna
  • Sakamakon harin bam da sojojin sama su ka kai a karamar hukumar Igabi, an rasa ayyuka a jiya
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta yi alkawarin yin jawabi, rundunar sojojin sama ba su ce uffan ba tukuna

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Kaduna - Mutane da-dama ake tsoron sun mutu a sakamakon wani bam da ake zargin sojojin sama sun saki a jihar Kaduna.

A safiyar Litinin, Daily Trust ta kawo rahoto cewa jirgin sojojin saman Najeriya ya saki bam a kan wasu masu taron maulidi.

Hakan ta faru ne kwanaki kadan bayan wani jirgin Kenya ya yi hadari a kan iyaka.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama hadimin Abba Gida-Gida da wani kan laifi 1 tak

Bam ya kashe 'Yan maulidi a Kaduna

Wannan abin takaici ya faru ne ga wasu mutane da ke garin da ake kira Tudun Biri da ke karamar hukumar Igabi a jihar Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Zuwa yanzu babu cikakken labarin abin da ya faru, amma ana zargin mutane akalla 30 su ka mutu a sanadiyyar harin bam din.

Mazauna Tudun Biri sun shaidawa jaridar cewa da kimanin karfe 9:00 na dare abin ya faru a ranar Lahadi ana taron maulidi.

Yadda abin ya faru ga masu maulidi

“Su na taron Maulidi (bikin murnar haihuwar Annabi Muhammad SAW), sai jirgin saman ya jefo bam
Nan take abin ya yi sanadiyyar mutane fiye da 30.”

- Mazaunin Kaduna

Ana tsoron adadin wadanda su ka rasu a harin sojojin saman zai iya zarce haka nan gaba a sakamakon yawan wadanda aka jikkata.

Kara karanta wannan

NDLEA ta gano katafaren gonar da ake noman wiwi a Sokoto, ta cafke mutum daya

Me sojoji da gwamnatin Kaduna su ka fada?

Da aka tuntubi Samuel Aruwan, ya shaida cewa za a kira taron manema labarai a gidan gwamnati da karfe 10:00 na safiyar yau.

Mista Samuel Aruwan ya ce za a yi jawabi na musamman a gidan gwamnati bayan an yi zaman majalisar tsaro a game da batun.

Zuwa yanzu babu wani jawabi da ya fito daga bakin rundunar sojojin saman Najeriya.

Yaki da rashin tsaro a Jihar Kaduna

A 'yan kwanakin nan rahoto ya zo cewa dubun gungun wasu miyagun mutanen da ke garkuwa da Bayin Allah ta cika a jihar Kaduna.

Rundunar ƴan sandan jihar ta samu nasarar yin caraf da su a wani sumame bayan sun dauki lokaci su na karbar kudin fansan mutane.

Asali: Legit.ng

Online view pixel