Shugaban Ma’aikatan Tsaro: Abubuwa 7 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Manjo Janar C.G Musa
Shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya nada Manjo Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon shugaban ma'aikatan tsaro don maye gurbin Janar Lucky Irabor.
DUBA NAN: Bibiyi shafin Legit.ng Hausa a kafar TikTok. Kada ka bari bidiyo mai daukar hankali ya wuce ka!
Shugaban kasa Tinubu ya amince da yi wa shugabannin tsaro ritaya nan take sannan ya sanar da madadinsu.
![Shugaban ma'aikatan tsaro Shugaban ma'aikatan tsaro](https://cdn.legit.ng/images/1120/7dbd5e5607e8009f.jpeg?v=1)
Asali: Facebook
Legit.ng ta tattaro muhimman abubuwa game da sabon shugaban ma'aikatan tsaron.
Ranar haihuwarsa
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an haifi Musa a ranar 25 ga watan Disambar 1967 a jihar Sokoto da ke arewa maso yammacin Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Jiharsa
Ya kasance dan arewa Kirista daga karamar hukumar Zangon Kataf da ke kudancin jihar Kaduna.
Karatu
Musa ya yi karatunsa na firamare da sakandare a jihar Sokoto.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/2998a6ec257e7676.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Janar Taoreed Abiodun Lagbaja: Abubuwa 6 Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Sabon Shugaban Hafsan Sojoji
Ya yi Difloma a faddin tsaro daga jami'ar Lagas, Difloma a bangaren dabarun tsaro a China da sauransu.
Shiga soja
Musa ya samu shiga makarantar sojoji ta NDA Kaduna a 1986 inda ya samu horo na tsawon shekaru biyar.
Laftanal na biyu a rundunar sojojin kasa
A watan Satumban 1991 ya shiga aikin sojan Najeriya a matsayin laftanar na biyu a rundunar sojojin, daya daga cikin sashi mafi wahala a rundunar soji.
Kwamandan bataliyar tsaron runduna ta 73
Ya kasance babban jami'in horarwa/ayyuka sashi na 81, hedkwata, ya kasance babban kwamandan Bataliya ta 73, Mataimakin Daraktan Ayyuka a Sashen Tsare-tsare na rundunar sojoji.
Kwamandan Sashi na 3 OP LAFIYA DOLE
Musa kasance kwamandan sashi na 3 OP LAFIYA DOLE, Kwamandan Sashe na 3 na rundunar hadin gwiwa a yankin tafkin Tchad, ya kuma rike mukamai da dama da ba a ambace su ba, PM News ta rahoto.
![](https://cdn.legit.ng/images/360x203/552ab5a1feddd52b.jpeg?v=1)
Kara karanta wannan
Shugaban Kasa Bola Tinubu: Cikakkun Sunayen Hafsoshin Tsaro, Manyan Kwamandojin Fadar Shugaban Kasa Da Sauransu
A 2021, ya kuma rike shugabancin Operation Hadin Kai da ke yaki da yan ta’adda a Arewa maso gabas.
Sabon shugaban hafsan soji: Abubuwan da ya kamata ku sani game da Janar Lagbaja
A wani labarin, Legit.ng ta kawo a baya cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana Janar Taoreed Abiodun Lagbaja a matsayin sabon shugaban hafsan sojojin Najeriya a ranar Litinin, 19 ga watan Yuni..
Ana ganin Janar Lagbaja na daya daga cikin janarori da suka san kan aiki sosai a rundunar sojojin Najeriya.
Asali: Legit.ng