Mutum 7 'yan gida daya sun mutu bayan cin nama suya da ruwan lemon jus

Mutum 7 'yan gida daya sun mutu bayan cin nama suya da ruwan lemon jus

  • Wasu iyalai sun bakunci lahira bayan da suka ci suya da mai gidan ya sayo a kasuwa
  • Rahoto daga jihar Abia ya bayyana cewa, akalla mutane bakwai ne suka mutu bayan cin naman
  • Biyu daga cikin iyalan sun tsira, kuma suna karbar kulawar asibiti a Asibitin Tarayya na Umuahia

Abia - Wasu iyalai mutum bakwai sun mutu bayan sun ci suyan kasuwa da ruwan jus a wani yankin Umuahia, babban birnin jihar Abia, Daily Trust ta ruwaito.

Lamarin ya faru ne a Umueze Umuakanu da ke karamar hukumar Umuahia ta Arewa a jihar.

Rahotanni sun ce, dukkan iyalan, ciki har da iyalan da suka zo hutu sun ci suyan wanda mai gidan, Mista Jessey, ya saya ya kawo gida.

Mutum 7 'yan gida daya sun mutu bayan cin nama suya da ruwan lemon jus
Suya | Hoto: lovepik.com
Asali: UGC

An ce sun fara amai bayan sun ci naman da ake zargin yana dauke da guba.

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya sakamakon kashe tsohon ɗan kwallon Nigeria da aka yi a rikicin Jos

Yanzu haka mutum ​biyu da suka tsira a cikin iyalan suna karbar magani a Asibitin Tarayya dake Umuahia, yayin da aka ajiye mamatan a dakin ajiye gawa na asibitin.

A halin da ake ciki, gwamnatin jihar Abia ta ce ta samu rahoto kan abin bakin cikin da ya faru.

A cikin wata sanarwa da Kwamishinan yada labarai, Cif John Okiyi Kalu ya fitar, ya ce Gwamna Okezie Ikpeazu ya umarci hukumomin asibitin da su kula da mutanen da suka tsira wajen jinya da kuma fitar da matattun don tabbatar da cikakken bincike.

Gwamnatin ta kuma yi kira ga 'yan kasa da mazauna yankin da su ci gaba da taka tsantsan wajen sayen abinci tare da ci gaba da bin doka.

Hayakin janareto ya hallaka mutane 7 'yan gida daya a jihar Osun

Kara karanta wannan

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

A baya Premium Times ta ruwaito cewa, an tsinci gawar wasu mutane bakwai 'yan gida daya a cikin dakunansu a karamar hukumar Apomu ta jihar Osun, ranar Talata 17 ga watan Agusta.

Rundunar 'yan sandan Osun ta ce ana zargin hayaki daga janareto ne sanadin mutuwarsu, amma sakamakon binciken gawa zai tabbatar da musabbabin mutuwar tasu.

Yemisi Opalola, mai magana da yawun rundunar, ta ce akwai mutane takwas a dakuna daban-daban na gidan amma mutum daya ne kawai aka tarar yana numfashi.

Kisan Musulmai a Jos: Majalisar malamai ta ce kada Musulmai su dauki doka a hannu

A wani labarin, Majalisar Malamai/Dattawa ta Jihar Filato ta yi kira ga al’ummar Musulmi da ke Jos da kada su kai farmaki kan kowa don daukar fansa kan kisan da aka yi wa musulmai a kan hanyar Gada-biyu - Rukuba, cikin Karamar Hukumar Jos ta Jihar Filato.

Kara karanta wannan

An hallaka makiyaya 3 a wani sabon harin ramuwar gayyar 'yan bindiga a Kaduna

An kashe wasu Fulani matafiya musulmai a ranar Asabar a kan hanyarsu ta komawa jihohin Ondo da Ekiti bayan sun halarci wani hidiman addini a Bauchi, an kai musu hari inda aka kashe sama da 20, mutane da yawa sun ji rauni kuma kusan 10 sun bace.

A rahoton Daily Trust, ta ce wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren kungiyar, Ahmad Muhammad Ashir ya ce:

"Musulunci bai goyon bayan tashin hankali saboda haka bai kamata a kai hari ko kashe wani da sunan daukar fansa ba."

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.