Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga

  • Daga uku, dalibai 6 cikin 136 dake hannun yan bindiga sun kwanta dama
  • Gwamnatin jihar ta jaddada cewa ba zata biya kudin fansa ba
  • Yan bindiga na cigaba da cin karensu ba babbaka a jihar Neja

Neja - Da alamun yara shida cikin 136 na daliban makarantar Islamiyyar Salihu Tanko Islamiyya, dake Tegina jihar Neja sun mutu hannun yan bindigan da suka sace su.

An yi garkuwa da wadannan yan ta'alikai ne ranar 30 ga Mayu a makarantarsu dake Tegina, karamar hukumar Maru ta jihar.

Ance Shugaban makarantar, Abubakar Alhassan, ne ya bayyana cewa yan bindigan sun kirasa don sanar da shi mutuwar yaran.

Alhassan yace yan bindigan sun ce yaran sun mutu ne sakamakon rashin lafiya, kuma ayi gaggawan biyan kudin fansa don sake sauran daliban.

Wani mahaifi wanda 'yayansa bakwai na cikin wadanda aka sace ya tabbatar da wannan labari.

Kara karanta wannan

Matasa a jihar Delta sun kona Masallaci kurmus don yan bindiga sun kashe shugaban yan banga

Yan bindigan sun bukaci N200m, an biyasu N30m

Yan makarantar na tsare a sansanoni 25 a cikin daji, mutumin da aka tura don kai kudin fansa ga maharan ya bayyana.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kasimu Barangana, mutumin da ya dauki Naira miliyan 30 zuwa wurin barayin, ya ce an ajiye yaran a wurare 25 a cikin jejin da ke dauke da dubban ’yan bindiga masu dauke da makamai.

Barangana ya bayyana cewa ‘yan fashin na tsare da yaran sosai inda suke ankare da duk wani motsi a cikin jejin.

Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga
Bayan sama da watanni biyu, daliban Tegina 6 sun mutu hannun yan bindiga
Asali: UGC

Yaushe zasu sako daliban?

Mutumin yace ba zai iya faɗin ranar da masu garkuwa zasu sako yaran ba, kawai a cigaba da addu'a Allah ya dawo da su lafiya.

Yace:

"Mu cigaba da addu'ar dawowar yaran mu cikin ƙoshin lafiya amma ba zai iya faɗin ranar da zasu sako su ba saboda yanzun suna neman mashin guda biyar a matsayin wata fansa."

Kara karanta wannan

Hawaye sun kwaranya yayin da ‘yan bindiga suka harbe sojoji 7 har lahira a Katsina

Ɓarayin sun cutar dakai yayin da kake hannunsu?

Barangana ya bayyana cewa yan bindigan sun kyautata masa yayin da yaje dajin, sun kula da shi yadda ya kamata.

Yace:

"Lokacin da nake cikin dajin tare da masu garkuwa da mutane, sun kula da ni yadda ya kamata, ana bani abinci isasshe. Da zan dawo suka bani dubu 11,000 in yi kuɗin mota."

Asali: Legit.ng

Online view pixel