Namijin Gwamna Ya Bi Sojoji Zuwa Wurin ‘Yan Bindiga Har An Ceto Wanda Aka Sace

Namijin Gwamna Ya Bi Sojoji Zuwa Wurin ‘Yan Bindiga Har An Ceto Wanda Aka Sace

  • Mai girma Dikko Umaru Radda ya kai ziyara zuwa garin Safana domin kaddamar da tsarin bada tallafi
  • Ana tsakiyar taron sai aka samu labarin ‘yan ta’adda za su yi barna, dole jami’an tsaro su ka shirya masu
  • Gwamna Dikko Umaru Radda yana kallo jami’an tsaro da dakarun ‘yan sanda su ka ceto wani matashi a daji

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada.

Katsina - A ranar Asabar Gwamna Dikko Umaru Radda, ya shiga cikin jami’an tsaro domin bankado wani shiri da ‘yan bindiga ke yi.

Sanarwa ta fito daga gidan gwamnatin Katsina cewa Mai girma Dikko Umaru Radda ya bi dakarun sojoji zuwa kauyen Zakka a Safana.

Gwamnan Katsina
Gwamna Dikko Ummaru Radda Hoto: @Miqdad_Jnr
Asali: Twitter

A wannan yunkuri da jami’an tsaron su ka yi, Gwamna Dikko Umaru Radda ya ganewa idonsa yadda aka ceto wani mai shekara 33.

Kara karanta wannan

Sarkin Kano ya yi wata magana mai jan hankali kan tsohon ministan sadarwa Sheikh Isa Pantami

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dikko Umaru Radda ya je Safana

Sakataren yada labaran gwamnan Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed ya sanar da haka a wani jawabi da aka fitar a shafin Twitter a jiya.

Malam Ibrahim Kaula Mohammed ya ce gwamna ya je karamar hukumar Safana ne domin kaddamar da wani shirin tallafawa marasa karfi.

Jawabin ya ce mataimakin shugaban majalisar dokokin jihar Katsina ya kawo tsarin.

Yadda abin ya faru da Gwamna Radda

Ana garin Safana tare da tawagar gwamna sai Kaula Mohammed ya ce aka samu labarin ‘yan bindiga za su kai hari ga mutanen yankin.

Da kimanin karfe 1:00 na rana da aka samu labari, sai Dikko Umaru Radda ya bar wajen taron bada tallafin, ya shiga sahun jami’an tsaro.

"Gwamna da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa sun bi wata rundunar hadin gwiwa, kunshe da ‘yan sanda, dakarun Operation Hadarin Daji, sjojin kasa da ‘yan sa-kai domin aukawa ‘yan ta’adda a dajin Zakka, kafin miyagun su iya kai ga tsauni.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano ya bayyana gaskiyar zaman Abba 'dan NNPP kafin hukuncin kotun koli

Bayan an yi ba-ta-kashi da bindigogi na kusan mintuna 30, an yi namijin kokari wajen ceto wani mai shekara 33. ‘Yan ta’addan sun yi nasarar tserewa ba tare da rauni ba bayan sun yi watsi da danyen aikin da su ka shirya."

- Ibrahim Kaula Mohammed

Gwamna Radda wanda yake son magance matsalar tsaro ya bukaci a kai wanda aka ceto zuwa asibiti saboda miyagun sun harbe shi a kafa.

Sojojin sun kashe mutane a Kaduna

Ana da labari Muhammadu Sanusi II ya yi wa al’umma ta’aziyyar rayukan Musulman da aka rasa a garin Kaduna a harin sojojin kasa.

Khalifan Tijjaniyan yana fata hukumomi za su yi bincike domin an dauki matakan da suka dace a kan wadanda su ka yi wannan danyen aiki.

Asali: Legit.ng

Online view pixel