Kotu Ta Ci Tarar Gwamnan Arewa Miliyan 500 Kan Zargin Take Hakkin Dan Takara a Zabe

Kotu Ta Ci Tarar Gwamnan Arewa Miliyan 500 Kan Zargin Take Hakkin Dan Takara a Zabe

  • Kotu ta ci tarar Gwamna Yahaya Bello har naira miliyan 500 kan zargin take hakkin dan takarar gwamna a jam'iyyar SDP
  • Dan takarar na SDP, Murtala Ajaka ya shigar da kara kotu kan neman kariya daga Gwamna Yahaya Bello
  • Wannan na zuwa ne bayan gudanar da zaben gwamna a jihar a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Babbar Kotun Tarayya ta ci tarar Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi miliyan 500 kan zargin take hakkin dan Adam.

Ana zargin Yahaya Bello da take hakkin dan takarar jam'iyyar SDP, Murtala Ajaka wanda ya yi takara a zaben gwamnan jihar.

Kotu ta ci tarar Yahaya Bello miliyan 500 kan zargin take hakkin dan Adam
Kotun Tarayya ta yi hukunci a karar Murtala Ajaka na jihar Kogi. Hoto: Yahaya Bello.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke?

Kara karanta wannan

Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a shari'ar neman tsige gwamna mai ci, ta ba da dalilai

Ajaka ya yi takara da dan takarar jam'iyyar APC, Usman Ododo wnda ya lashe zaben a ranar Asabar 11 ga watan Nuwamba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin yanke hukuncin, Mai Shari'a, Inyang Ekwo ya umarci Bello ya fito ya ba da hakuri kan take hakkin Ajaka, cewar Vanguard.

Ekwo ya umarci jami'an tsaro da su kare lafiyar Ajaka da dukiyarsa a jihar Kogi da Abuja har ma da sauran wurare a Najeriya.

Wannan umarni na kariya ya kuma hada da kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zaben da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Mene alkali ya ce kan karar?

Alkalin ya ce:

"Wannan umarni ne na dakatar da cin mutunci da kama wa ko harbi ko cin zarafin wanda ke karar da kuma dukiyarshi."

The Nation ta tattaro cewa a ranar 11 ga watan Yuli, Ajaka ya shigar da kara kan neman kariya daga kotun.

Kara karanta wannan

"Akwai kotun Allah": Martanin jama'a bayan kotu ta yanke hukunci a shari'ar Abba da Ado Doguwa

Ajaka ya maka Yahaya Bello da Kwamishinan 'yan sanda a jihar Kogi da hukumar DSS da kuma Babban Sifetan 'yan sanda.

Rikicin ya fara ne tun bayan hana Ajaka takara a APC wanda hakan ya saka shi koma wa jam'iyyar SDP.

Yahaya Bello ya kirkiri sabuwar ma'aikata

A wani labarin, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya kirkiri sabuwar sabuwar ma'aikata a jihar ana makwanni kadan kafin ya bar mulki.

Gwamnan ya kirkiri ma'aikatar jin kai da walwalar jama'a don rage radadin talauci a jihar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel