Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Neman Tsige Gwamna Mai Ci, Ta Ba da Dalilai

Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama a Shari'ar Neman Tsige Gwamna Mai Ci, Ta Ba da Dalilai

  • Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a jihar Legas ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jam'iyyar LP a matsayin gwamna
  • Kotun ta kuma yi fatali da korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun PDP da APC da zargin kawo wasan barkwanci a cikin dimukradiyya
  • Ta ce kasancewar Otti dan jam'iyya ne ko akasin haka hurumin jami'yya ce kafin zabe wanda babu ruwanta a ciki

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Legas - Kotun Daukaka Kara ta raba gardama a hukuncin shari'ar zaben Gwamna Alex Otti na jihar Abia.

Kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Alex Otti na jam'iyyar LP a matsayin wanda ya lashe zabe, Legit ta tattaro.

Kara karanta wannan

Rikicin shari'ar Kano: An kai karar Gwamna Yusuf Majalisar Dinkin Duniya, bayani ya fito

Kotu ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan Abia
Kotun ta yi hukunci kan shari'ar zaben gwamnan jihar Abia. Hoto: Alex Otti.
Asali: Facebook

Wane hukunci kotun ta yanke na shari'ar Abia?

Har ila yau, ta yi watsi da korafe-korafen 'yan takarar jam'iyyun PDP da APC saboda rashin isassun hujjoji.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kotun da ke zamanta a jihar Legas ta yanke hukuncin ne a yau Asabar 2 ga watan Disamba inda ta ce 'yan takarar APC da PDP barkwanci su ke son shigar wa dimukradiyya.

Ta kuma ce matsalar kasancewa dan jam'iyya ko sabanin haka wannan matsala ce ta jami'yya kafin zabe.

Vanguard ta tattaro cewa kotun ta tabbatar da nasarar Gwamna Otti ne saboda zaben ya yi dai-dai da tsarin dokar hukuncin zabe.

Kotun ta kuma kori karar dan takarar PDP da jam'iiyarsa kan korafinsu na na'urar tantancewa ta BVAS.

Ta ce dan takarar da jam'iyyarsa ba su gabatar da kwararan hujjoji ba game da tuhumar da su ke yi ba musamman a kan matsalarsu.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta raba gardama kan shari'ar zaben dan Majalisar PDP, ta bayyana mai nasara

Gwamna Otti na gudanar da mulkinsa daga kauye

A wani labarin, Gwamna Alex Otti na jihar Abia ya ci gaba da gudanar da mulkinsa daga kauyensu bayan hawa mulki.

Tun bayan hawanshi karagar mulki, Otti bai taba amfani da sabo ko tsohon gidan gwamnatin jihar ba yayin da yake mulki daga kauye.

Gwamnatin da ta shude ta gina sabon gidan gwamnati inda ta kaddamar da shi kwanaki biyu kafin barin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Online view pixel