Kwanaki Kadan Kafin Barin Kujerar Mulki, Gwamnan APC Ya Kirkiri Sabuwar Ma’aikata, Ya Fadi Dalili

Kwanaki Kadan Kafin Barin Kujerar Mulki, Gwamnan APC Ya Kirkiri Sabuwar Ma’aikata, Ya Fadi Dalili

  • Yayin da ake saura makwanni kadan da barin mulki, Gwamna Yahaya Bello ya sake kirkirar ma’aikata a jihar Kogi
  • Gwamnan ya kirkiri ma’aikatar jin kai da walwalar jama’a don taimakon marasa karfi da kuma rage radadin talauci a jihar
  • Wannan na zuwa bayan zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 11 ga watan Nuwamba wanda za a rantsar a watan Janairun 2024

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, kwararren editan siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi – Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya sake kirkirar sabuwar ma’aikata a jihar yayin da ya ke shirin barin mulki.

Gwamnan ya kirkiri ma’aikatar Jin Kai da Walwala a jihar don taimakon marasa karfi a fadin jihar baki daya, cewar Tribune.

Kara karanta wannan

Innalillahi: Allah ya yi wa shugaban karamar hukumar Gombe rasuwa da yammacin yau

Gwamnan APC ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata kwanaki kadan kafin barin mulki
Gwamna Yahaya Bello ya sake kirkirar sabuwar ma'aikata a Kogi. Hoto: Yahaya Bello, Usman Ododo.
Asali: Facebook

Yaushe Yahaya Bello ya bayyana haka?

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da hadiminsa a bangaren yada labarai, Oogwu Muhammad ya fitar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yahaya Bello ya kaddamar da ma’aikatar ce yayin fara shirin Gwamnatin Tarayya na tallafi karkashin ma’aikatar Tarayya ta Jin Kai da Walwala.

Gwamna ya yabawa Gwamnatin Tarayya kan shirye-shiryenta musamman a kokarin rage radadin talauci a kasar.

Wane yabo ya yi kan Ododo?

Wannan na zuwa ne yayin da ya rage saura makwanni kadan gwamnan ya bar kujerar mulki.

Gwamna Yahaya Bello ya ce:

“Gwamnati na ta yi duk mai yiyuwa don tabbatar da kirkirar wannan ma’aikata ta jin kai da walwalar jama’a.
“Wannan tallafi zai taimakawa marasa karfi da kudade naira dubu 20 don rage musu halin wahala.
“Wannan shiri zai taimaka wurin tabbatar da tsarin mu na cire dukkan masu fama da talauci kunci.”

Kara karanta wannan

Yayin da ake jimamin hari kan masu Maulidi, dan Majalisa ya kaddamar da shirin kulawar lafiya kyauta

Gwamnan ya kuma ba da tabbacin cewa gwamna mai jiran gado, Usman Ododo zai ci gaba da ayyukan alkairi da ya fara.

Bello ya ce Ododo zai kuma yi hadaka da Gwamnatin Tarayya don kawo ci gaba ga mutanen jihar Kogi, cewar Leadership News.

Yahaya Bello ya biya kudin WAEC a Kogi

Kun ji cewa, Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi ya biya wa dalibai dubu 15 kudin jarabawar WAEC.

Wannan na zuwa ne yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a jihar a ranar 11 ga watan Nuwamba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel