Sambisa: Sojoji Sun Kashe Kwamandan ISWAP da Ya Kware a Hada Bama Bamai

Sambisa: Sojoji Sun Kashe Kwamandan ISWAP da Ya Kware a Hada Bama Bamai

  • A ruwaito cewa, Mallam Muhammad, babban kwamandan ISWAP mai kula da hada bama-bamai ya gamu da ajalinsa a Sambisa
  • Dakarun Operation Desert Sanity III da na Operation Hadin Kai ne suka kashe Mallam Muhammad a ranar 14 ga watan Mayun 2024
  • Kwamandan na 'yan ISWAP ya kware a hada bama-bamai na kunar bakin wake, da na sakawa a mota, da kuma na dasawa a kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Sambisa, jihar Borno - Dakarun sojojin Najeriya sun kashe Mallam Muhammad, babban kwamandan ISWAP mai kula da hada bama-bamai na VBEID.

Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP
Borno: Sojoji sun kashe kwamandan ISWAP a dajin Sambisa. Hoto: @HQNigerianArmy
Asali: Twitter

An ce dakarun Operation Desert Sanity III da na Operation Hadin Kai ne suka kakkabe Mallam Muhammad a dajin Sambisa.

Kara karanta wannan

Rikicin Rivers: EFCC ta na neman gwamnan PDP ruwa a jallo? Gaskiya ta fito

Kwamandan ISWAP da ya iya hada bam

An ga bayan Muhammad ne a ranar 14 ga watan Mayu bayan jerin hare-hare da sojojin suka kaddamar a matsugunan ‘yan ta’addan a Ukuba da Njimia a karamar hukumar Bama.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kamar yadda Zagazola Makama ya ruwaito, kwamandan na ISWAP ya kware a hada bam din kunar bakin wake (PBVIED), da na sakawa a mota (VBIED), da kuma na dasawa a kasa (RSBIED).

An ce Muhammad ya jima yana tura kananan yara suna yin kunar bakin wake da tunanin cewar idan sun mutu za su shiga aljanna.

Sojoji na fatattakar 'yan ta'adda a Sambisa

An tattaro cewa ya yi amfani da bama-baman (PBVIED) a kan yaran da ya haifa guda uku, wadanda suka yi kunar bakin wake.

Majiyar tsaro ta shaidawa Zagazola Makama cewa dakarun sojin sun kama wata mota wadda take dauke da bam da ke da nufin farmakar sojojin.

Kara karanta wannan

Sambisa: Sojojin Najeriya sun fafata da Boko Haram, an kashe babban aminin Shekau

Duk da kalubalen bama-baman IED na kasa, sojojin na ci gaba da maida hankali da kara azama wajen fatattakar 'yan ta'addan da suka watsu a dajin Sambisa.

Sojoji sun kashe aminin Shekau

A wani labarin, mun ruwaito cewa sojojin Najeriya sun samu nasarar kashe Tahir Baga, daya daga cikin manyan jagororin mayakan Boko Haram a Borno.

An kashe Tahir Baga, wanda aminin marigayi Shekau ne a lokacin da sojojin suka kai wani samame a dajin Sambisa, a wani atisaye na kakkabe 'yan ta'adda daga dajin.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel