Tashin Hankali: Ana Jimamin Kashe Bayin Allah a Wurin Maulidi, Wani Abu Ya Fashe a Jihar APC

Tashin Hankali: Ana Jimamin Kashe Bayin Allah a Wurin Maulidi, Wani Abu Ya Fashe a Jihar APC

  • Yayin da ake jimamin abinda ya faru a Kaduna, wata babbar mota ɗauke da man Dizel ta fashe ta kama da wuta a jihar Legas
  • Hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce jami'an sun shawo kan yanayin da aka shiga
  • Har yanzu babu wani bayani a hukumance kan abinda ya haddasa fashewar tankar ranar Litinin da safe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Lagos - Wata babbar motar dakon mai ɗauke da man dizel ta fashe kuma ta yi filla-filla a yankin Ojota da ke jihar Legas ranar Litinin, 4 ga watan Disamba, 2023.

Tanka ta fashe a jihar Legas.
Mota Dakon Mai Makare da Man Dizel Ta Fashe, Ta Yi Filla-Fila a Jihar Legas Hoto: thenation
Asali: UGC

Hukumar kula da zirga-zirgan ababen hawa ta jihar Legas, (LASTMA), ce ta tabbatar da aukuwar ibtila'in a shafinta na manhajar X wadda aka fi sani da Tuwita.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun kama hadimin Abba Gida-Gida da wani kan laifi 1 tak

Hukumar ta kuma bayyana cewa tuni ta tura jami'anta zuwa wurin domin kai agajin da ya kamata da kuma shawo kan lamarin a kan lokaci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta wallafa a shafinta cewa:

"An samu fashewar tanka wacce ta kama da wuta a Ojota, jami'an ceto na jihar Legas da kuma na hukumar LASTMA sun isa wurin domin yin abinda ya dace."
"Muna bukatar matafiya da sauran direbobi su yi haƙuri a wannan lokacin."

Har kawo yanzu da muke haɗa maku wannan rahoton, ba a bayyana maƙasudin abin da ya haddasa fashewar babban motar ba.

Wane hali ake ciki bayan faruwar lamarin?

Haka nan kuma daga bisani hukumar kashe gobara da ayyukan ceto ta jihar Legas (LSFRS) ta babbatar da faruwar lamarin yau Litinin da safe.

Ta yi bayanin cewa a halin yanzun jami'an ceto da sauran hukumomin ba da agaji sun yi nasarar shawo kan lamarin, komai ya fara dawowa daidai a yankin.

Kara karanta wannan

An yi asarar dukiya sakamakon gobara a masallaci da shaguna a Jigawa

Hukumar LSFRS ta wallafa a shafinta na manhajar X cewa:

"Yanayin da aka shiga a yankin Ojota na karkashin kulawa bayan wata babbar mota ɗauke da man dizel ta fashe kuma ta kama da wuta."

Rundunar sojin ƙasa ta ɗauki laifin kai harin bam a Kaduna

A wani rahoton kun cewa daga ƙarshe, rundunar sojin kasa ta Najeriya ta ɗauki laifin harin bam ɗin da aka kai kan bikin Maulidi ranar Lahadi a Kaduna.

Kwamandan runduna ta ɗaya, Manjo VU Okoro, ya yi bayanin yadda jami'an soji suka yi kuskure yayin kai samame kan yan bindiga.

Asali: Legit.ng

Online view pixel