Zanga-Zanga Ta Barke a Filato Bayan Kotu Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisun Tarayya na PDP

Zanga-Zanga Ta Barke a Filato Bayan Kotu Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisun Tarayya na PDP

  • Rahotanni sun bayyana cewa zanga-zanga ta barke a manyan garuruwan Jos/Bukuru, biyo bayan hukuncin kotu na kwace kujerun 'yan majalisun tarayya na PDP
  • Masu zanga-zangar sun nuna rashin goyon bayan hukuncin kotun na soke nasarar da ‘yan takarar PDP suka samu a zaben majalisar dattawa da ta wakilai da ya gabata
  • Ibrahim Yakubu, wakilin masu zanga-zangar, ya bukaci majalisar shari’a ta kasa da ta duba tare da yin nazarin hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

An gudanar da zanga-zanga a manyan wurare cikin kwaryar Jos/Bukuru da ke jihar Filato a yankin Arewa ta tsakiya a ranar Larabar da ta gabata, a matsayin martani ga hukuncin da kotun daukaka kara ta yanke na korar mambobin jam'iyyar PDP daga majalisar dokokin kasar.

Kara karanta wannan

Kotun daukaka kara ta gama aiki, ta yanke hukunci kan nasarar dan majalisar tarayya na PDP

Masu zanga-zangar wadanda galibinsu matasa ne da mata, sun nuna rashin jin dadinsu ga hukuncin kotun daukaka kara da ya soke nasarar da ‘yan takarar PDP suka samu a zaben majalisar dattawa da ta wakilai da ya gabata.

Zanga-zanga a Jos
Masu zanga-zangar sun bukaci majalisar shari'a ta kasa ta sake duba hukuncin kotun daukaka karar zaben Hoto: IndependentNGR
Asali: Twitter

Ya kamata majalisar shari’a ta kasa ta duba hukuncin kotu - Yakubu

Masu zanga-zangar dai na dauke da kwalaye daban-daban domin nuna damuwarsu da rashin amincewa da hukuncin kotu da ya yi watsi da sakamakon kuri'unsu da suka jefa a rumfunan zabe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Da yake jawabi ga masu zanga-zangar a sha tale-talen Maraba, karkashin inuwar kungiyar masu ruwa da tsaki ta Filato, Ibrahim Yakubu, ya bukaci majalisar shari’a ta kasa da ta duba tare da yin nazarin hukuncin da kotun daukaka karar ta yanke.

Kotun daukaka kara da ke zamanta a Abuja ta soke nasarar dukkan ‘yan takarar majalisar tarayya karkashin jam'iyyar PDP a zabubbukan da aka yi, saboda rashin mutunta umarnin kotu na shirya zabukan fitar da gwani a matakin gundumomi da jiha na jam’iyyar.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da zanga-zangar kwana 30 har sai Tinubu ya yi murabus

Kotun zabe ta kwace kujerun 'yan majalisar PDP a Filato

Kun ji cewa, kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majalisun jiha da na tarayya ta ƙwace kujerun mambobin majalisar dokokin jihar Filato uku na jam'iyyar PDP, kamar yadda jaridar Legit Hausa ta ruwaito.

Wadanda Kotun ta tsige sun hada da, Remvyat Nanbol, Agbalak Adukuchill da Happiness Akawu da ke wakiltar mazaɓun Langtang ta tsakiya, Rukuba/Iregwe da Pengana a majalisar dokokin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel