Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da Zanga-Zangar Kwana 30 Har Sai Tinubu Ya Yi Murabus

Hukuncin Kotun Koli: Za a Gudanar da Zanga-Zangar Kwana 30 Har Sai Tinubu Ya Yi Murabus

  • Sakamakon hukunci koli, kungiyoyi 30 za su gudanar da zan-zanga ta nuna kin amincewa da mulkin Shugaba Bola Ahmed Tinubu
  • Kungiyoyin karkashin 'New Nigeria Diaspora Movement (CNNDM)', sun kuma sha alwashin ganin Tinubu ya yi murabus kafin kwanaki 30
  • Zanga-zangar a cewar kungiyar za a gudanar da ita a dukkanin kasashen duniya, musamman kasashen da shugaban kasar ya yi shirin zuwa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Akalla kungiyoyi 30 na 'yan Najeriya mazauna kasashen ketare, da ke karkashin kungiyar hadaka ta 'New Nigeria Diaspora Movement (CNNDM), su ka sanar da kudirinsu na gabatar da zanga-zanga mai taken "Zanga-zangar kwato Najeriya", da nufin tilasta Shugaba Tinubu ya yi murabus.

Kara karanta wannan

Babban Sarkin Yarbawa ya bayyana ma’anar tambarin da aka saba gani a hular Tinubu

Kungiyar ta kuma bukaci Kungiyar Tarayyar Turai (E.U.), kasar Burtaniya, Amurka, da wasu kasashe da su sanya dokar haramta biza ga alkalan Kotun Koli da suka yanke hukuncin karar zaben shugaban kasa, inda suka ayyana Tinubu a matsayin wanda ya yi nasara.

Shugaban kasa Bola Tinubu
Kungiyoyi 30 za su gudanar da zanga-zanga ta tsawon kwanaki 30 har sai Tinubu ya yi murabus Hoto: Bola Ahmed Tinubu
Asali: Twitter

Wannan kiran na hana biza ya hada har da iyalan alkalan, kamar yadda rahoton jaridar Legit ta ya nuna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani taron manema labarai da ya gudana a ranar Litinin, 6 ga watan Nuwamba, Jackson Ude, babban sakataren kungiyar hadakar, ya sanar da cewa CNNDM ta shirya gudanar da wannan zanga-zangar kuma tana maraba da duk wata kungiya da ke cikin Najeriya da ke son ayi da ita.

Kungiyar na sa ran zanga-zangar za ta gudana na tsawon kwanaki 30, tare da fatan za a kwaci kasar daga hannun Shugaba Tinubu kafin karshen wa'adin zanga-zangar.

Kara karanta wannan

Sarkin Legas ya bai wa Tinubu, Atiku da Peter Obi muhimmin shawara bayan hukuncin kotun koli

Ude ya ce:

Muna da yakinin cewa Mr Tinubu ba wai aringizon kuri'u a zaben shugaban kasa na 2023 kadai ya yi ba, hatta takardun ilimi, da zasu ba shi damar mulkar Najeriya bai mallaka ba. "
Tinubu ya yi takardun Jami'ar Jihar Chicago na bogi, da wannan kawai, ya aikata babban laifi na ha'inci da buga takardun bogi, wanda ya kamata a hukunta shi."
Kazalika, Tinubu mamba ne na wata tawagar masu fataucin miyagun kwayoyi da ke Amurka, kamar yadda binciken hukumar FBI ya nuna. Kenan, ya aikata laifuka da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi."

Babban sakataren kungiyar ya ci gaba da cewa:

“CNNDM ta amince da bukatar gudanar da zanga-zangar kwato Najeriya a fadin kasashen duniya domin bayyana wa kowa irin ta'addancin Bola Tinubu tare da bukatar murabus dinsa nan take."
“CNNDM ta amince ta taimaka wa kungiyoyi da ke cikin Najeriya domin shiga cikin wannan zanga-zangar wacce za a gudanar da ita na tsawon kwanaki 30, da nufin kwato Najeriya daga hannun Tinubu."

Kara karanta wannan

Jirgin ruwan N5.5bn: Abin da ’yan Najeriya suka shuka ake girba – Tsohon dan takarar shugaban kasa

Ude ya ce kungiyar hadakar ta sha alwashin ci gaba da matsin lamba har sai Bola Tinubu ya sauka daga kujerar shugabancin Najeriya.

Ya bayyana cewa sun yanke shawarar hada kan dukkan 'yan Najeriya da ke zaune a kasashen da Tinubu ya ke shirin zuwa domin gudanar da zanga-zanga, ta hanyar nuna zarge zargen da ake yi masa na buga takardun bogi da aikata laifukan da suka shafi fataucin miyagun kwayoyi, da cewar bai dace ya zama shugaban Najeriya ba.

Najeriya, Isra'ila da sauran kasashen da Amurka ba ta da jakadu

A wani labarin, gwamnatin kasar Amurka ta ce har yanzu ba ta da jakada a Najeriya, duk da irin ci gaban da aka samu na kawance a tsakanin kasashen biyu, kamar yadda Legit Hausa ta ruwaito.

Matthew Miller, mai magana da yawun ma'aikatar kula da harkokin kasashen waje na Amurka, da ke aiki karkashin sakataren Amurka na US 71s, Anthony Blinken, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a shafinsa na X (tsohuwar Twitter).

Kara karanta wannan

Shahararren lauya ya fada wa Atiku da Obi abin da za su yi bayan hukuncin kotun koli

Asali: Legit.ng

Online view pixel