Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisar PDP Uku a Jihar Filato

Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisar PDP Uku a Jihar Filato

  • Kotun zabe mai zama a Jos ta sauke yan majalisar dokokin jihar Filato guda uku na jam'iyyar PDP ranar Alhamis
  • Kwamitin alkalan Kotun ƙarƙashin mai shari'a Muhammad Tukur, ya ce Kotu ta tsige su ne saboda PDP ba ta da ikon tsayar da 'yan takara
  • Wannan hukunci na zuwa ne a daidai lokacin da ake dakon hukuncin Kotun kan zaben gwamnan jihar na ranar 18 ga watan Maris

Jos, Jihar Plateau - Kotun sauraron ƙararrakin zaben 'yan majalisun jiha da na tarayya ta ƙwace kujerun mambobin majalisar dokokin jihar Filato uku na jam'iyyar PDP.

Waɗanda Kotun ta tsige sun haɗa da, Remvyat Nanbol, Agbalak Adukuchill da Happiness Akawu da ke wakiltar mazaɓun Langtang ta tsakiya, Rukuba/Iregwe da Pengana a majalisar dokokin jihar.

Kotun zabe ta tsige karin mambobin majalisar dokokin jihar Filato.
Kotun Zabe Ta Kwace Kujerun 'Yan Majalisar PDP Uku a Jihar Filato Hoto: dailytrust
Asali: Twitter

A hukuncin da ta yanke a ranar Alhamis, kotun ta bayyana Daniel Ninbol Listic na jam’iyyar LP, Bako Ankala da Yakubu Sanda na APC da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka yi nasara.

Kara karanta wannan

Bidiyon Yadda Ganduje, Gawuna Suka Yi Murna Bayan Kotu Ta Tsige Abba Ya Yadu

Kwamitin alkalai bisa jagorancin mai shari’a Muhammad Tukur ya ce Kotu ta tsige ‘yan majalisar ne saboda ba PDP ta ɗauki nauyinsu ba, Daily Trust ta rahoto.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya ce hakan ta faru ne sakamakom ƙin bin umarnin Kotu na gudanar zaben gundumomi wanda zai ba PDP damar kafa halastaccen tsarin jam'iyya.

Ya kara da cewa PDP ba ta da tsari don haka ba ta da ikon ɗaukar nauyi da tsayar da ‘yan takarar da zasu shiga zabe ba.

Daga Ƙarshe Kotun ta umarci INEC ta janye shaidar cin zaɓen da ta baiwa yan majalisar PDP, kana ta miƙa wa sabbin waɗanda Kotu ta ce su suka ci zaɓe.

Kotu na shirin yanke hukunci kan zaben gwamna

Kotun ta yanke wannan hukunci ne yayin da ake dakon hukuncin da zata yanke game da zaben gwamnan Filato na ranar 18 ga watan Maris, 2023.

Kara karanta wannan

Kotun Zabe Ta Tsige Abba Gida-Gida Daga Kujerar Gwamnan Kano, Ta Faɗi Wanda Ya Ci Zaɓe

Jaridar Solabase ta tattaro cewa ɗan takarar gwamnan a inuwar APC, Dakta Nentawe Yiltwatda, shi ne ya ƙalubalanci nasarar gwamna Caleb Mutfwang na jam'iyyar PDP.

Hukumar zaɓe ta ƙasa mai zaman kanta (INEC) ta ayyana Muftwang a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Filato da ƙuri'u 525,299.

Hakan ya ba shi damar lallasa babban abokin hamayyarsa na jam'iyyar APC Yiltwatda, wanda ya tashi da ƙuri'u 481,370. Amma ya garzata ya kai ƙara Kotu.

Abba Gida-Gida Ya Tara Kwamishinoni da Hadamai, Ya Faɗa Musu Magana Mai Jan Hankali

Kuna da labarin Gwamnan Abba Kabir Yusuf ya bai wa kwamishinoni da hadiman da ya naɗa shawara bayan Kotu ta sauke shi.

Abba ya buƙaci su bar komai a hannun Allah kuma har yanzun yana da damar ɗaukaka ƙara zuwa Kotun sama.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Online view pixel