An Nada Farfesa Mohammed Matsayin Sabon Shugaban Jami'ar FUT Minna

An Nada Farfesa Mohammed Matsayin Sabon Shugaban Jami'ar FUT Minna

  • Jami'ar fasaha ta tarayya da ke Minna, ta sanar da nada Farfesa Abdullahi Mohammed a matsayin sabon shugaban jami'ar, fannin ilimi
  • Jami’ar, cikin wata sanarwa dauke da sa hannun Mrs Lydia Legbo, ta ce nadin shugaban zai fara daga ranar 7 ga Nuwamba, 2023, kuma zai kare nan da shekaru biyu
  • Farfesa Mohammed ya fara aikinsa a jami’ar a matsayin mataimakin lakcara a shekarar 2000, inda ya samu kwalin M.Eng., a shekarar 2003

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Kwamitin nade-nade da kara girma (A&PC) na jami’ar fasaha ta tarayya dake Minna, ya tabbatar da nadin Farfesa Abdullahi Mohammed a matsayin sabon shugaban jami’ar (Academic).

Jami’ar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar mai dauke da sa hannun shugabar sashen yada labarai da hulda da jama’a, Mrs Lydia Legbo, wacce jaridar Nigerian Tribune ta samun kwafinta a ranar Talata a Minna, inda ta ce an tabbatar da nadin ne a taron jami’ar karo na 87 da ya gudana a ranar Talata, 7 ga watan Nuwamba, 2023, a gidin majalisar jami'ar da ke Gidan Kwano.

Kara karanta wannan

Ana saura kwanaki 3 zaben gwamna, a karshe tsohon shugaban kasa ya bayyana wanda ya ke muradi

FUT Minna
Jami'ar FUT Minna ta tabbatar da Farfesa Abdullahi Mohammed a matsayin sabon shugaba (Academic) Hoto: Federal University of Technology, Minna.
Asali: UGC

Sanarwar ta ci gaba da cewa, Majalisar dattawan jami’ar, a yayin taronta na yau da kullum karo na 480 da ta gudanar a ranar Laraba, 26 ga Yuli, 2023, ta zabe shi a matsayin shugaba mai jiran gado, inda ta jaddada cewa sabon shugaban (Academic), Farfesa Abdullahi Mohammed, farfesa a 'Civil Engineering', an haife shi a ranar 28 ga watan Fabreru, 1972, a garin Lapai, karamar hukumar Lapai jihar Niger.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Madam Lydia Legbo, mataimakiyar magatakarda, ta ce Farfesa Mohammed ya halarci makarantar firamare ta Kobo daga 1977 zuwa 1983 da kuma sakandire ta Muhammadu Kobo da ke Lapai daga 1983 zuwa 1989, tare da jaddada cewa ya kammala karatunsa a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya samu fita da sakamako na kusa da kololuwa (Second Class, Upper) a shekarar 1998, kuma ya yi wa kasa hidima a kamfanin Zenith Engineers, jihar Kaduna, daga 1999 zuwa 2000.

Kara karanta wannan

‘Yan Majalisa za su yi binciken yadda ake saida Digiri kamar ruwan leda a Jami’a

Sanarwar ta kara da cewa Farfesa Mohammed ya fara aikinsa a jami’ar a matsayin mataimakin lakcara a shekarar 2000, inda ya samu kwalin M.Eng., a shekarar 2003, kamar yadda jaridar Tribune ta ruwaito.

Ya dakata da karatunsa bayan samun digirin digirgir a fannin fasahar gine gine ta hanyar amfani da kankare, a Jami'ar Tenaga Nasional, Malaysia, a cikin shekarar 2011.

A cewar sanarwar, sabon shugaban makarantar (Academic) ya rike mukamai daban daban da suka hada jami'in ba da shawara a fannin matakan karatu, jami'in jin dadin dalibai, mai kula da ayyukan kammala karatu na sashe, mai kula da dalibai masu karatun PGD da kuma shugaban sashe.

A cewar Mrs. Legbo, sabon shugaban jami'ar (Academic) ya kasance har zuwa sabon nadin nasa a matsayin Darakta a fannin tsare-tsaren ayyukan Ilimin jami'ar.

Bugu da kari, an bayyana Farfesa Abdullahi Mohammed a matsayin mamba na kungiyar injiniyoyi ta Najeriya (NSE), wacce ke da rajista da cibiyar kula da harkokin injiniyanci a Najeriya (COREN), kuma ya yi aiki a matsayin mai ba da gudummawa ga COREN da kungiyar jami'o'i ta kasa (NUC) a fannin bincike da amince wa da shirye-shiryen da jami'o'i za su rinka gudanar wa a kasar.

Kara karanta wannan

Tashin hankali yayin da walkiya ta kashe dalibai suna tsaka da buga kwalla a Anambra

Ta ci gaba da cewa, baya ga yin aiki a kwamitin Asusun Bunkasa Fasahar Man Fetur (PTDF) don zaben wadanda za a sanya a shirin bayar da tallafin karatu zuwa kasashen waje, ya wallafa littattafai sama da 50 na kasa da kasa tare da kula da daliban da suke karatun digiri na farko da na biyu, PGD, M.Eng., da PhD.

Nadin, wanda zai fara aiki daga ranar 7 ga Nuwamba, 2023, zai kasance na tsawon shekaru biyu a matakin farko, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

'Yan bindiga sun kai hari gefen FUT Minna

A baya-bayan nan, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda wasu tsagerun 'yan bindiga suka kai wani hari yankin Gidan-Kwano, gefen jami'ar fasaha ta tarayya (FUT) da ke garin Minna, babbar birnin jihar Neja.

Maharan sun halaka mutum daya sannan sun yi garkuwa da wasu mutane biyu a harin, jaridar Daily Trust ta rahoto.

Asali: Legit.ng

Online view pixel