‘Yan Majalisa Za Su Yi Binciken Yadda Ake Saida Digiri Kamar Ruwan Leda a Jami’a

‘Yan Majalisa Za Su Yi Binciken Yadda Ake Saida Digiri Kamar Ruwan Leda a Jami’a

  • Shugaban Majalisar dokokin Legas ya amince kwamiti ya binciki zargin da ake yi na sayen shaidar digiri a jami’ar LASU
  • Mudashiru Obasa ya bayyana cewa za a binciki lamarin ko ba domin komai ba illa saboda gudun sunan jami’ar jihar ta baci
  • Hadimin Rt. Hon. Obasa ya ce za a gayyaci Kwamishina da Shugabannin jami’ar Legas domin a gano gaskiyar lamarin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M. Malumfashi ya shafe shekaru ya na kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Lagos - Majalisar dokokin jihar Legas, ta ce za ta gayyaci Kwamishinan harkokin ilmi mai zurfi da shugaban jami’ar LASU domin bincike.

Punch ta ce ‘yan majalisa za su yi bincike ne a game da zargin da ake yi na cewa ana biyan kudi domin sayen takardar shaidar zir a LASU.

Kara karanta wannan

Ga mari, ga tsinka jaka: APC ta yi wa Peter Obi raddi kan batun shari’ar zaben 2023

A sakamakon haka za a gayyato Tolani Akibu, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello da sauran shugabannin jami’ar jihar domin jin ta bakinsu.

Jami'ar LASU
Ana zargin ana saida Digirin Jami'ar LASU Hoto: lasu.edu.ng
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Digirin kudi: Shugabannin LASU a Majalisa

Kwanan nan rahoto ya fito cewa mutane na biyan tsakanin N2m da N3m domin a ba su shaidar digiri daga LASU ko da ba su taba shiga aji ba.

Ana zargin cewa tsadar takardar digirin bogin da ake fansa ya danganta da wahala da tsaurin irin kwas din da mutum ya zama a jami’ar.

Za ayi binciken digiri a Majalisa da LASU

Sahara Reporters ta ce jami’ar ta LASU ta fitar da jawabi ta bakin Oluwayemisi Thomas-Onashile cewa za ayi bincike babu rufa-rufa.

Mai taimakawa shugaban majalisar jihar Legas wajen yada labarai, Eromosele Ebhomele ya fitar da jawabi cewa za ayi cikakken bincike.

Majalisar ta ce akwai alamun tambaya game da tushen labarin domin an san gidan jaridar da yin karya da yaudarar mutane tun ba yau ba.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP da kujerarsa ke tangal-tangal ya nemi afuwar talakawan jiharsa kan abu 1 da ya faru

Abin da ya sa za a binciki digirin LASU

A dalilin haka ne Mai girma Rt. Hon. Mudashiru Obasa ya ce za a gayyaci wadanda abin ya shafa su zo majalisa domin a ji ta bangarensu.

Shugaban majalisar dokokin yake cewa yin hakan ne zai wanke jami’ar daga zargi.

Obasa wanda shi kan shi tsohon dalibin LASU ne, ya ce kwamitin harkar ilmi zai yi binciken ne saboda gudun a bata sunan jami’ar a Duniya.

ASUU za ta buga da gwamnati a jami'a

An ji labari shugaban kungiyar ASUU ya ce gwamnati na neman karbe 40% na rangwamen da ake yi wa dalibai wajen biyan kudi a jami'o'i.

Farfesa Emmanuel Osodeke ya fadawa gwamnati cewa jami’o’i ba cibiyoyin tatsar kudi ba ne, saboda jin za a rika zaftare kudin da su ka tara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel