Jiga-jigan PDP da Su ka Taya Bola Tinubu Murnar Nasara Kan Atiku a Kotun Koli

Jiga-jigan PDP da Su ka Taya Bola Tinubu Murnar Nasara Kan Atiku a Kotun Koli

  • Ana samun wasu ‘ya ‘yan jam’iyyar PDP da su ke yi wa Bola Ahmed Tinubu murna game da nasarar da ya samu a kotun koli
  • Zuwa yanzu akalla Gwamnonin jihohin hamayya 2 sun je yi masa barka ko kuwa sun aikawa shugaban kasa sakon murna
  • Nyesom Wike wanda ya samu kujerar Minista a sakamakon karya jam’iyyarsa ta PDP a zaben 2023 ya ji dadin hukuncin jiya

M. Malumfashi ya kan kawo labarai na Hausa musamman na siyasa, addini, wasanni da al’ada

Abuja - Idan da rai da lafiya kuma aka cigaba da tafiya a haka, Bola Ahmed Tinubu ne shugaban Najeriya akalla har zuwa Mayun 2027.

A ranar Alhamis, Kotun koli ta tabbatar da nasarar Mai girma shugaban kasan a karshen shari’ar zabensa da Atiku Abubakar da Peter Obi.

Magoya baya da shugabannin APC har da Muhammadu Buhari sun yi maraba da sakamakon da alkalan kotun koli su ka yi a jiya.

Kara karanta wannan

Mutane 2 kaɗai Su ka fi Ni Yi wa Tinubu Kokari,Na Cancanci Kujerun Ministoci – Rarara

Bola Tinubu
APC ta yi nasara a kotun koli Hoto: Bola Ahmed Tinubu, Douye Diri, Ademola Adeleke
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A rahoton nan, Legit ta kawo wasu daga cikin ‘yan adawa na jam’iyyar PDP da su ka nuna farin cikinsu ga hukuncin da kotun koli ta zartar.

1. Nyesom Wike

Tsohon gwamnan Ribas ya nemi tikitin shugaban kasa a PDP, amma daga baya ya yaki Atiku Abubakar har ta kai ya zama Minista a gwamnatin APC.

Wike ya ce bai da-na-sanin goyon bayan Bola Tinubu a zaben shugaban kasa.

2. Douye Diri

Duk da ya na cikin gwamnonin jam’iyyar hamayya ta PDP, Douye Diri ya taya Bola Ahmed Tinubu murnar nasarar da ya samu bayan kwanaki 171 a kotu.

Nan da ‘yan kwanaki Douye Diri zai nemi tazarce a zaben gwamnan jihar Bayelsa.

3. James Ibori

James Ibori ya na cikin jagororin jam’iyyar PDP da su ka ziyarci Mai girma shugaban kasa a fadar Aso Villa domin taya shi murnar nasarar da ya samu.

Kara karanta wannan

"Abun Takaici"Jam'iyyar PDP Ta Maida Zazzafan Martani Kan Rashin Nasarar Atiku a Kotun Ƙoli

Ibori ya yi gwamna na shekaru takwas a Delta, kuma har gobe ya na da ta-cewa a PDP.

4. Ademola Adeleke

Ba a bar Gwamnan jihar Osun watau Ademola Adeleke a baya wajen taya Tinubu murnar yin nasara a kotun koli ba, duk da cewa ya yake shi a zaben 2023.

Adeleke ya na cikin wadanda su ka ba Atiku Abubakar goyon baya sosai a zabensa.

5. Reno Omokri

Tun da ake shari’ar zaben shugaban kasa, Reno Omokri bai da kwarin gwiwar cewa jam’iyyarsa za ta yi nasara wajen tunbuke gwamnatin APC a kotu.

Tsohon hadimin na Goodluck Jonathan ya ji dadi da Peter Obi na LP bai kai labari ba.

Kotun koli ta ba Tinubu gaskiya

Atiku Abubakar da Peter Obi sun sake kunyata a kotu a shari’ar zaben shugaban kasa duk wahalar da ‘Dan takaran PDP ya sha a kasar Amurka.

Kotun koli ta ce babu inda dokar kasa ta nuna sai an samu 25% na kuri’un birnin Abuja kafin a hau mulki, ikirarin da lauyoyin Peter Obi su ka yi.

Asali: Legit.ng

Online view pixel