Rarara: Mutum 2 kaɗai Su ka fi Ni Kokari a Tafiyar Tinubu, Na Cancanci Kujerun Ministoci

Rarara: Mutum 2 kaɗai Su ka fi Ni Kokari a Tafiyar Tinubu, Na Cancanci Kujerun Ministoci

  • Dauda Adamu Kahutu ya kira taron manema labarai, ya yi magana a kan Bola Ahmed Tinubu da kotu ta tabbatar a mulki
  • Shararren mawakin siyasan ya bayyana cewa gwamnatin Muhammadu Buhari ta damalamala komai kafin ta bar shugabanci
  • Rarara ya ce a irin taimakon da ya bada, ya cancanci a ba shi kujerun Ministoci da wasu ma’aikatu ko hukumomi na tarayya

M. Malumfashi ya kan kawo labarai na Hausa musamman na siyasa, addini, wasanni da al’ada

Abuja - Dauda Adamu Kahutu ‘Rarara’ ya kira taron manema labarai, a nan ya tofa albarkacin bakinsa a game da mulkin Bola Ahmed Tinubu.

A bidiyon da su ke ta yawo a kafofin sadarwa na zamani, Alhaji Dauda Adamu Kahutu da aka fi sani da Rarara ya soki mulkin Muhammadu Buhari.

Kara karanta wannan

Jiga-jigan PDP 4 da Su ka Nuna Farin Ciki da Nasarar Tinubu Kan Atiku a Kotun Koli

Rarara ya bayyana cewa ya bada gudumuwa sosai wajen kafuwar gwamnatocin APC yayin da ake taya Bola Tinubu murnar samun nasara a kotu.

Rarara
Rarara, Muhammadu Buhari da Abdullahi Ganduje Hoto: www.bbc.com/hausa
Asali: UGC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gudumuwar Rarara a gwamnatin APC

Mawakin ya yi ikirarin za a iya cewa gudumuwarsa wajen kafa gwamnati ta kai akalla 10% zuwa 20%, saboda haka ya cancanci a jinjina masa.

A dalilin haka Dauda Adamu Kahutu ya ce idan za a kafa gwamnati, ya dace a ba shi kujerun ministoci ko da biyu ne domin ya kawo mutanensa.

Haka zalika idan za a zakulo shugabannin ma’aikatu na gwamnatin tarayya, mawakin siyasar ya na ganin to kyau a ba shi kujeru goma.

Mutum 2 su ka fi Rarara taimakon Tinubu

A wajen yakin zaben Bola Ahmed Tinubu da aka yi, Rarara ya ce manyan ‘yan siyasa biyu kurum su ka fi shi taimakawa jam’iyyar APC mai mulki.

Kara karanta wannan

Rarara: Tsohon Hadimi Ya Mayar Wa Mawaki Raddi Mai Zafi Saboda Caccakar Mulkin Buhari

Wadannan ‘yan siyasa ba kowa ba ne a cewarsa sai tsofaffin gwamnonin jihohin Katsina da Kano; Aminu Bello Masari da Abdullahi Umar Ganduje.

Na yi Buhari tsakani da Allah, a gwamnatin Buhari ko shi (Buhari) bai kai ni ba shi gudumuwa ba.
Na farko shi ne Aminu Bello Masari domin tun ana saura shekaru biyu ayi zabe ya ce ka da in canza layi, Bola Tinubu za ayi.
Na biyu kuma Dr. Abdullahi Umar Ganduje saboda da aka zo maganar zaben nan, ya fi kowa zakalkalewa a kai.

Nadin mukaman Tinubu

Shekara 4 da barin Majalisa, ana da labari cewa yaron Sanatan Katsina ta Kudu, Abu Ibrahim ya samu mukami a gwamnatin shugaba Bola Tinubu.

Masu noman kaji a Katsina sun ji dadin ba Muhammad Abu Ibrahim kujerar Hukumar NADF

Asali: Legit.ng

Online view pixel