Ba Gaskiya Ba Ne Batun Cewa Hukumar DSS Ta Saki Nnamdi Kanu

Ba Gaskiya Ba Ne Batun Cewa Hukumar DSS Ta Saki Nnamdi Kanu

  • Wani rahoto na baya-bayan nan ya ƙaryata iƙirarin cewa an saki Nnamdi Kanu, shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB)
  • Wani faifan bidiyo da ya yaɗu a soshiyal midiya ya nuna wata mata tana bayar da bayanai kan batun sakin Nnamdi Kanu
  • Bincike ya tabbatar da cewa Kanu, wanda a halin yanzu yake fuskantar shari'a, har yanzu yana tsare, kuma faifan bidiyon kan sakinsa na ƙarya ne

Wani rahoto da ya fito ya tabbatar da cewa maganganun da ake a kafafen sada zumunta waɗanda ke tabbatar da sakin shugaban masu fafutukar kafa ƙasar Biyafara (IPOB), Nnamdi Kanu, ƙarya ne.

An tabbatar da hakan ne a wani rahoton binciken da Dubawa.org ya fitar a ranar Laraba, 25 ga Oktoban 2023.

Ba gaskiya ba ne batun sakin Nnamdi Kanu
Shugaban yan kungiyar IPOB, Nnamdi Kanu Hoto: Marco Longari
Asali: Getty Images

Shugaban ƙungiyar ta IPOB, wanda ke fuskantar ƙalubalen shari’a, dai an kori takwas daga cikin tuhume-tuhume 15 da ake yi masa a watan Afrilun 2022, sauran bakwai kuma an kore su a watan Oktoban 2022.

Kara karanta wannan

Assha: Yadda Rashin Jituwa Ta Sanya Magidanci Ya Halaka Matarsa da Wuka

Sai dai, rundunar ƴan sandan farin kaya har yanzu ba ta saki Kanu ba daga tsare shin da take yi.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A ina aka yaɗa batun sakin Nnamdi Kanu?

Wani mai amfani da sunan "Billionaire Blogger" a Facebook, ya sanya wani faifan bidiyo inda wani mutum da wata mata suka yi iƙirarin cewa an sako shugaban na IPOB.

Cikin murna ta bayyana cewa:

"Allah mai iko. Sun saki Nnamdi Kanu, sun saki Nnamdi Kanu."

Matar wacce ke zaune a ƙasar Faransa kamar yadda aka gani a faifan bidiyon, ta nuna goyon bayanta tare da taya shugaban ƙungiyar ta IPOB murna.

Hakazalika, ta tabbatar da cewa shugaban ƙungiyar ta IPOB zai zama shugaban ƙasar Najeriya nan gaba. Ta ƙarfafa gwiwar masu amfani da Facebook waɗanda suka kalli bidiyon da su yaɗa shi.

Kara karanta wannan

Tsshin Hankali Yayin da Jami'an Tsaro Suka Yi Artabu da Kasurgumin Dan Ta'adda a Babban Birnin Jihar Arewa

An sake iƙirarin sakin Kanu

A wani ɓangare na faifan bidiyon, wani mutum ya bayyana inda ya ƙarfafa maganar cewa an saki Kanu.

Ya ƙara da cewa kotun ta yanke hukuncin sakin shugaban ƙungiyar ta IPOB, inda ya ce kama shi ya saba wa dokokin ƙasa saboda kasancewarsa ɗan ƙasa biyu.

Dokubo Ya Shawarci Tinubu Kan Sakin Kanu

A wani labarin kuma, tsohon shugaban tsagerun yankin Niger-Delta, Alhaji Mujahid Dokubo Asari, ya shawarci Shugaba Tinubu da ka da ya saki Nnamɗi Kanu.

Asari ya bayyana cewa sakin shugaban na ƙungiyar IPOB ba zai haifar da komai ba, face ƙara tayar da zaune tsaye a yankin Kudu maso Gabashin Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng

Online view pixel